Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano (KSPWB) ta sha alwashin kwashe daukacin maniyata aikin Hajjin bana guda 6,000, adadin da hukumar alhazai ta kasa ta bai wa Jihar Kano a wannan shekara.
Hukumar ta bayyana hakan ne ganin yadda bara aka bar wasu maniyata masu ya-wa da ba su iya sauke farali ba.
Tsohon babban sakataran hukumar alhazai na Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayana haka a ranar Laraba da ta gabata a lokacin wani taron bita ga mahajjata wanda aka yi a harabar sansanin alhazan.
Taron bitan ya kwashe tsawon ana yi wa maniyatan Jihar Kano a cibiyoyi da ke kananan hukumomi 44 na jihar, wanda aka kammala da nuna aikin hajji da yadda ake dawafi na kewaya dakin Ka’aba.
A karshe dai hukumar alhazan ta Jihar Kano ta bayyana cewa a ranar 3 ga wannan wata maniyatan Kano za su fara tashi zuwa kasa mai tsarki, domin sauke farali na wannan shekara.
Sai dai kuma a wani labarin na daban, saban gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) ya ba da sanarwa rushe shugabancin hukumar alhazai ta Jihar Kano tare da nada saban baban sakataran zartarwa na hukumar, Alhaji Laminu Baba Danbaffa da kuma Alhaji Lawan Yusuf a matsayin saban shugaban hukumar alhazan Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp