Hafsoshin sojin kasashen Afirka ta Yamma da suka yi taro a birnin Accra na kasar Ghana, sun ce ECOWAS za ta mayar da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar ta ko wace hanya.Â
Yayin da yake jawabin bude taron hafsoshin, wanda sh ine karo na biyu da suke yi domin nazari a kan matakan da ya dace a dauka wajen amfani da karfi a kan sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, kwamishinan tsaro da zaman lafiya, Abdul Fatau Musah ya ce abin da ke gaban su shi ne ganin an dawo da mulkin farar hula a kasar.
- Gobarar Tsibirin Maui Ta Bata Amincewar Da Jama’a Suka Yi Da Gwamnatin Amurka
- Jami’ai 3 Da Sojoji 22 ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Neja -DHQ
Shugabannin ECOWAS suka bai wa hafsoshin sojin kasashensu umarnin nazari da kuma bada shawara a kan matakan da ya dace a dauka idan bukatar amfani da karfin soji, sakamakon bijirewar sojojin da suka yi juyin mulkin.
Wannan matsayi na shirin amfani da karfin na ci gaba da fuskantar adawa daga wasu kasashe da kuma kungiyoyin jama’a ciki har da Amurka da Rasha wadanda ke bukatar ci gaba da daukar matakan diflomasiyya domin warware matsalar.
Rahotanni sun ce taron kungiyar kasashen Afirka (AU) a kan juyin mulkin na Nijar bai kai ga daukar matsayin bai daya ba sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu tsakani kasashen da suka halarci taron.
Firaministan da sojojin Nijar suka nada, Ali Lamine Zeine, ya ce tuni suka fara shirin mayar da mulki a kasar, yayin da majiyoyi da dama ke cewa sojojin sun bayyana bukatar tattaunawa da ECOWAS.