Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya bayyana cewar jami’an tsaro za su fara farautar mutanen da ke rike da takardun kammala karatun digiri na bogi a fadin Nijeriya.
Ministan, ya bayyana hakan a Abuja, yayin taron masu ruwa da tsaki a bangaren ilmin Nijeriya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Wutar Lantarki A NijeriyaÂ
- Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Yanar Gizo Na Kyautata Rayuwar Jama’a
Ministan ya kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin gudanar da muhimman sauye-sauye a bangaren ilmi ta hanyar kaddamar da wata taswira mai fannoni 13.
Ya kara da cewar, matukar ana son gudanar da cikakken tsari a fannin ilmi, musamman a matakin firamare da karamar sakandare, ya zama wajibi a samar da sahihan bayanai da za su bunkasa koyon sana’o’in dogaro da kai da zasu taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
A farkon watan Janairun 2024 ne, ministan ya bayyana cewar jami’an tsaro zabsu fara farautar ‘yan Nijeriya da ke rike da takardun kammala karatun digirin bogi daga kasashen ketare.
Ya bayyana irin wadannan mutane a matsayin masu laifi.
“Bana tausayin irin wadannan mutane. A maimakon haka ma ina yi musu kallon wani bangare na gungun masu laifi daya kamata a kama”.
Ministan Ilmin ya kara da cewar, gwamnatin tarayya za ta dakatar da amincewa da takardun kammala karatun digiri daga karin kasashe irin su; Uganda da Kenya da Jamhuriyar Nijar.