Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi gargadin cewa, ba za a amince da kawo tangarda ga harkokin tsaro a gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba.
Ribadu ya bayyana haka ne a taron babban Kwanturolan Hukumar Kwastam, CGC, a Abuja ranar Laraba, inda ya jaddada aniyar shugaban kasar na kawar da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, da sauran kalubalen tsaro.
- Tankar Mai Ta Sake Yin Hatsari A Jigawa
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Biyan Bashin Waɗanda Aka Tsare A Gidan Gyaran Hali
A cewar Ribadu, manyan tsare-tsare na gwamnati kan kawar da kalubalen tsaro sun kai ga kashe daruruwan ‘yan bindiga a kullum, lamarin da ya tilasta wa da dama tserewa zuwa kasar Chadi.
“saboda haka, shugaban Chadi ya ayyana yaki da ‘yan bindigar da ke tserewa zuwa kasar.
“Za mu tabbatar da tsaron kasar nan, za mu gyara ta, kuma dagaske muke,” in ji shi.
Ribadu ya tabbatar da cewa, gwamnati na aiki tukuru don ganin an samu ingantaccen yanayi, wanda ke da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.