• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari – Fintiri

by Muh'd Shafi'u Saleh
2 years ago
Fintiri

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, na jihar Adamawa, ya tabbatar wa al’ummar jihar kudurin da ya rataya a wuyan gwamnatinsa na ganin ta gurfanar da mutanen da suka hada baki,l da dakatacce kwamishinan hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar, Hudu Yunusa Ari, kan rawar da ya taka a babban zaben 2023.

Fintiri, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa jama’ar jihar jawabi a ranar Litinin, ya ce “mu na iya mu kare tsarin zabenmu da dimokuradiyya daga cin zarafin da bai kamata ba.

  • Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
  • Bikin Bazara Da Ke Fadada A Duniya Alama Ce Ta Mu’amala Da Fahimtar Juna Tsakanin Wayewar Kan Kasar Sin Da Wayewar Kai Daban-Daban

“Ita kanta kotun Koli a cikin hukuncinta ta yi Allah-wadai da matakin da Hudu Ari ya dauka, ta ce matsayin wani aiki ne na ‘rashin hankali da aikata laifuka’ wanda ya jefa harkar dimokradiyya cikin kunya da dimauta” inji gwamnan.

Haka kuma, gwamna Fintiri, ya nuna gamsuwa da yadda alkalai a matakai daban-daban na kotuna suka jajirce wajen warware rudun da aka kawo a matakai daban-daban tare da fitar da hukuncin da ya dace da al’ummar jihar Adamawa.

Ya ce “hukuncin da kotun koli na ranar 31/01/2024, ya kawo karshen duk wata hayaniyar zaben 2023 a Adamawa, kwanakin karya da yaudara sun kare, lokacin farfagandar karya da maganganun son zuciya sun shude.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

“Dole na yabawa hukumar zabe INEC da ta tsaya tsayin daka ta kare mutunci da kimarta ta gujewa son zuciya, lokacin da Kwamishina Hudu Ari, ya aikata son zuciya da rashin bin ka’idar doka” inji Fintiri.

Gwamna Ahmadu Fintiri, ya ce duk da yanzu ba lokacin takara ba ne, amma jihar Adamawa jiha ce ta jam’iyyar PDP, kamar yadda aka gani lokacin zabuka da kuma a yadda ta kasance a kotuna, an lura da yadda mutanen suka yi magana da katunan zabe.

“Shaidar hakan ita ce sabuwar nasarar da PDP ta samu a zaben dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazabar karamar hukumar Mayo-Belwa, mu na kara godiya ga masu kada kuri’a da suka kara sanya nasara a kan hukuncin da kotun koli ta yanke” ya jaddada.

Gwamna Ahmadu Fintiri, ya kuma baiwa jama’ar jihar tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da musu hidima, tsare-tsare da kyautata rayuwa, ilimi kyauta, samar da kiwon lafiya, kayayyakin more rayuwa a birane da karkara, karfafa mata da matasa da sauransu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
Manyan Labarai

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya
Labarai

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Next Post
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa

An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa

LABARAI MASU NASABA

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.