Jam’iyyar adawa ta NNPP da ta lashe zaben gwamnan Kano, ta ce za ta yi nazarin rahoton mika mulki da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike mata.
Gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ta gabatar da rahoton mika mulki na shekarar 2023 ga zababben Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.
A wata ‘yar gajeriyar ganawa da aka yi a dakin taro na gidan gwamnatin Kano, Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya jaddada aniyarsa na ganin an samu sauyi ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma bukaci gwamnati mai jiran gado da ta yi nazari kan rahoton mika mulki tare da bayar da ra’ayoyinsu idan ya cancanta, domin ya yaba wa mambobin gwamnatin mai barin gado bisa samar da kaso uku na rahoton da ya kunshi dukkan sassan jihar.
A nasa jawabin, zababben gwamnan Jihar Kano wanda shugaban kwamitin mika mulki na jam’iyyar NNPP, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, ya wakilta, ya nuna cewa kwamitinsa zai kai rahoto ga gwamna mai jiran gado sannan ya dawo da duk wani abin dubawa idan akwai.
“A wannan lokacin, muna da sa’o’i 105 kacal kafin mu mika mulki a Jihar Kano a hukumance, don haka muka himmatu wajen ganin mun yi komai a kan lokaci domin amfanin Kano da al’ummarta.”
A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai game da bikin rantsuwa bayan an cimma wasu yarjejeniyoyin da aka yi tsakanin gwamnati mai barin gado da mai jiran gado.