A daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris 2023, jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna na neman hadin gwiwa da sauran jam’iyyun siyasar jihar domin kayar da jam’iyyar APC mai mulki.
Idan za a tuna jam’iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, da kujeru uku na Sanata da kujerun majalisar wakilai da dama a Jihar Kaduna.
- Kamfanin Ericsson: Kamfanonin Sadarwa Na Kasar Sin Sun Gaggauta Rungumar Fasahar 5G
- Wani Bikin Kaddamarwa Mai Muhimmanci
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Felix Hassan Hyet, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Kaduna.
Yayin da yake yabawa al’ummar jihar bisa gagarumin goyon bayan da suka nuna a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya na kananan hukumomi 23, Hon. Hyet ya nemi karin goyon baya a lokacin zaben gwamna da ke tafe.
A cewarsa, kayen da jam’iyyar APC mai mulki ta sha a jihar alama ce ta kin amincewa da gwamnatin APC a Jihar Kaduna gaba daya da mutanen jihar suka yi.
“Ina mika godiya ta ga mutanen Jihar Kaduna da suka fito rumfunan zabe domin zaben jam’iyyar PDP, ina mai alfahari da cewa an nuna tasirin da yakinin al’ummar Jihar Kaduna ta hanyar sakamakon zaben.
“A karon farko a tarihi, PDP ta lashe kujerun sanatoci uku, da kuma mazabu 10 daga cikin 16 na tarayya na jihar, fiye da zaben 2019.”
Hyet ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP a jihar ba ta bar wani abu ba don tabbatar da cewa PDP ta yi nasara a zabe mai zuwa yayin da ya jaddada cewa za su hada kai da sauran jam’iyyu don cikar burinsu.