Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe ta lashe mazabar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan na jam’iyyar APC.
Wannan dai na zuwa ne bayan kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar.
- Firaministan Sin Ya Bukaci A Karfafa Ci Gaba Da Kuma Daidaita Farashin Kayayyaki
- Zaben 2023: ‘Yan Daba Sun Sace Na’urar BVAS 8 A Delta Da Katsina
Sakamakon zaben shugaban kasa, a rumfar da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya jefa kuri’arsa, ya nuna jam’iyyar PDP tare da dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya doke abokin takarar sa a jam’iyyar APC, Bota Ahmed Tinubu, da tazara mai yawa.
Rumfar zaben wadda take a makarantar Firamaren Katuzu mai lamba 001B, inda sakamakon ya nuna dan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri’u 107, yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPC ya samu kuri’u 41, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP mai kuri’u 186.
Sakamakon Majalisar Dattawa a rumfar (001B) ya nuna jam’iyyar APC ta samu yawan kuri’u 301, jam’iyyar PDP 37 sai na jam’iyyar NNPP kuri’u biyu (2) kacal.
Haka zalika, dan takarar kujerar Majalisar Wakilai, a rumfar zaben, jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben da yawan kuri’u 219 fiye da na jam’iyyar APC mai kuri’u114.
A daya bangaren kuma, a daya rumfar zaben (001N-Z), a cikin makarantar Firamaren Katuzu, sakamakon shugaban kasa ya nuna PDP ce a kan gaba da kuri’u 84, fiye da APC mai kuri’u 52, sai NNPP mai 25. Yayind APC ta samu kuri’u 155, PDP 15 a takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe.
Har wala yau, a takarar Majalisar Wakilai, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 103, yayin da APC ta samu 58, NNPC kuma 5.
Har wala yau, a rumfa mai lamba 001A a cikin makarantar Firamaren Katuzu, dan takarar shugaban kasa, tare da jam’iyyar sa sun samu kuri’u 113, APC 94, NNPC 26, inda dan takarar LP ya samu kuri’u 1 kacal.
Haka kuma jam’iyyar APC ta samu kuri’u 207, PDP 24, NNPC 7 a wannan rumfar (001A) a takarar Sanatan Arewacin Yobe. Inda kuma PDP ta samu kuri’u 134, APC 89 a takarar Majalisar Wakilai a wannan rumfar.