A wannan makon mun kawo muku ra’ayoyin ‘yan Nijeriya ga ‘yan siyasar da suka lashe zabukkan da aka yi da kuma wadanda suka sha kasa.
Kabo Idris Saminu
Ni dai abin da zance gaskiya ya kamata dukkanmu,mu hankalta mu zo mu gina kasar tare bazai da ana nufin dan ka fadi gwamnati ka koma gefe kana yarfe da bata gwamnati ka dauka daidai kake rusa kasar kake ta yadda koda can gaba ka karbe ta babu makawa sai kafi na baya shan wahala kai kuma da kaci karka dauka abokanan karawar ka wai makiya ne gare wani gyara da suke fada lallai akwai shi ya kamata a hada hannu da hannu domin a ceci kasar ga baki dayan mu
Abubakar Mohammed Joda
Ni a ra’ayina mabiya da magoya baya sun fi bukatar shawara. Kada wadanda gwaninsu ya sami nasara su mayar da nasararsu abin izgili ga wadanda suka fadi. Domin wuta ce ke ci a zukatan wadanda suka fadi zabe, ina jan hankalin duk ‘yan Nigeria su guji antayawa wutar da ke ci a zukatan mutane man fetur. Musamman a irin wannan lokaci.
Umar Ibrahim Umar
Dama Allah ya tsara duk wanda za su ci da wanda za su fadi muna taya wanda suka samu nasara muna musu fatan Alheri Allah ya basu ikon sauke nauyin daya rataya a kan su wanda suka fadi Kuma muna fatan za su dauki kaddara su barwa Allah ikonsa kuma su tara 2027 idan muna raye, Allah ya sa mu dace Amin.
Muhammed Abdullahi Dankano daga Unguwar Sarkin Lakwaja.
Toh, Alhamdulillahi, anyi zabe lafiya kuma an kammala lafiya. Wadanda za su lashe zabe, Allah Ya basu nasarar lashe zaben, haka kuma wadanda Allah Ya kaddara za su fadi, sun fadi.
Shawara ta ga wadanda suka lashe zaben shi ne su yi kokari su cikawa talakawa alkawarin da suka daukar musu na inganta rayuwarsu. Ko basu cika alkawuran duka ba, toh, su yi iyakar bakin kokarinsu,yafi ace basu cika kwata kwata ba. Domin a gaskiya idon jama’a na kansu kwarai da gaske.
An yi zabe na ban mamaki a Nijeriya duk da cewa akwai kurakurai da ba a rasa ba. Jama’a sun fito kwai da kwarkwatansu suka zabi wadanda suke so su wakilcesu a matakan mulki daban-daban.
Kamata ya yi suma wadanda aka zaban su baiwa marada kunya,su kyautatawa jama’a ba tare da nuna bambancin jam’iyya, addini ko yare ba. Su rungumi kowa da kowa. A yanzu kowa nasu ne. A gaskiya jama’a na cikin wani hali na kuncin rayuwa.
Saboda haka nake kira ga wadanda suka ci zaben da su taimakawa jama’a don fidda su daga kangin talauci da suka tsinci kansu ciki.
Haka kuma su ji tsoron Allah wajen gudanar da mulki wajen sauke nauyin da Allah da kuma jama’a suka dora musu.
Ga wadanda ba su yi nasara kuwa ba, su tuna cewa Allah Shi ke bada mulki ga wanda ya so,a kowani lokaci kuma a lokacin daya ga dama. Saboda haka, nake kira ga wadanda suka fadi, da su rungumi kaddara, su tuna cewa Allah shike bayarwa. Su dauki lamarin cewa yadda Allah Yaso kenan.
Duk abinda kaga ka samu, Allah ne, idan ka rasa Allah ne. Sai dai shawarata ga yan siyasa shine suji tsoron Allah kuma kyautata mu’ammalarsu da jama’ar da suke mulka kuma su koyi darasi ga yan siyasar baya” inji Dankano.
Danjuma Danfulani Lakwaja
Shawarwarin da zan baiwa ‘yan siyasar da suka lashe zaben da ma wadanda suka sha kasa.
“Alhamdulillahi, an kammala zaben cikin kwanciyar hankali da lumana,sai da dan abinda ba za a rasa ba.
Yanzu kam, shawarata ga wadanda suka lashe zaben shi ne idan sun kama aiki gadan-gadan, su yi kokari su fuskanci jama’ar da suka fito suka sha rana, suka yi dafifi a layukan zabe suka zabe su. A gaskiya, jama’a na cikin wani Hali na hukuba.
Sau da yawa a baya, an sha yiwa talaka romon baka, an shafa masa mai a baki, ana ta yaudararsu da karyayyaki, amma aka gagara cika masa alkawuran da aka daukar masa.
Babu asibiti,babu ruwan sha, babu abinci, babu kudi, kai duk wani abubuwan more rayuwa,talaka bashi dasu.
Shawarata karshe, shi ne ga hukumar zabe ta INEC, musamman ma shugabannin hukumar, su rika jin tsoron Allah su rika kamanta gaskiya da adalci. Idan ana adalci, duk wanda yaci zabe, a bashi zabensa ba tare da an danne shi.A hakan sai a samu zama lafiya.
Shugabannin hukumar zabe ta INEC sunyi alkwarin zasu gudanar da zabuka masu tsafta, amma aka samu akasin haka a wasu wuraren, bayan sun dauki alkawarin zasu yi adalci . A don haka nake kira ga hukumar data gyara a nan gaba.
Allah ya babu zama lafiya a Nijeriya, ya bamu shugabanni na gari masu tausayin talaka”,a cewar Danfulani.
Mannur Umar Mai Litattafe, Gusau, ya yi kira ga wadanda suka samu nasara zabe da su ji tsoran Allah wajen ba mutane hakin su wadanda suka zabe su.kuma su sani fa cewa, Allah zai tambaye su abubuwan da suka aikata lokacin sina mulki, kuma su tafi da kowa da kowa jan tafiyar da Shugabancin su banda nuna bambamci a tsakanin al’ummar su.
Wadanda suka fadi zabe kuwa su yi hakuri idan kuma zuciyar su taba iya hakuri sai su tafi kotu don neman hakin su idan Allah ya sa suna da rabo sai su yi nasara.amma banda rikici tsakanin su.
Malam Auwal Umar,Gusau ya yi kira ga wadanda suka ci zabe,da su sani cewa, Allah ne ya basu da dabara su bace, dan haka suyi kawoma alumma ayyukan ci gaba, kuma su tabbatar da cewa, yanzu alhakin al’umma na kanasu kuma yanzu babu bambancin siyasa a tsakanin su wajen tafiya da kowa da kowa.
Wadanda su basu samu nasara ba su barma Allah kuma ya dauka haka ne yafi alhairi a wajen su.idan zabe mai zuwa yazo na 2027 Idan rai sai su sake tsayawa, idan da rabo sai Allah ya basu.