• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

by El-Zaharadeen Umar
2 days ago
in Labarai
0
Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsohon Sanatan Shiyyar Daura, Sanata Ahmad Babba Kaita ya bayyana cewa zaben 2027 yaki ne zai kasance tsakanin talakawa da ake mulka da kuma shugabanni masu mulki.

Sanatan ya bayyana haka ne a lokacin da suke amsar ‘yan takara daga jam’iyyar adawa ta PDP su 268 da suka hada da kansiloli da ciyamoni da kuma ‘yan majalisun jiha a zaben 2023.

  • Fafutikar Makinde Da PDP Wajen Neman Mulki A 2027

Haka ya jaddada cewa al’umma ta gaji da irin bakin mulkin da ake yi mata, saboda haka, alamu sun nuna cewa yakin dole sai an gwabza shi tsakanin bangarorin biyu na talakawa da masu mulki.

Zuwa yanzu dai jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Katsina na ci gaba da fuskantar tawaye daga ‘ya’yanta, domin shiga sabuwar hadaka da za a tunkari jam’iyya mai mulki a Jihar Katsina da kasa baki daya.

Kamar yadda suka bayyana, tsaffin ‘yan takara da suka hada da wadanda suka yi takarar majalisar jihar a zaben 2023 mutum 25 daga cikin talatin 34 a karkashin jam’iyar PDP.

Labarai Masu Nasaba

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

Jagoran wannan sabuwar tafiya kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da tsaffin ‘yan takarar suka je ofishinsa domin jadadda goyon bayansu kan sabuwar tafiya.

Shi ma da yake magana a madadin sauran ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a zaben 2023, Hon. Jamilu Yahaya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda aka nisantar da su daga al’umma wanda su ne ke yin zabe.

A nashi bangaren, shugaban ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi, Hon. Yasir Ibrahim ya ce sun shiga wannan hadaka ne saboda irin yaudarar shugabanci da aka yi masu a tsohuwar jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice.

Da yake nasa tsokaci, shugaban tsaffin ‘yan takarar kansiloli na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Hon. Usman Aminu ya bayyana cewa su 225 ne suka amince da wannan sabuwar tafiya, amma yana kokarin ganin sauran ma sun shiga an yi da su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 2027INECZabe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Next Post

Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

Related

Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama
Manyan Labarai

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

20 minutes ago
Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC
Manyan Labarai

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

1 hour ago
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano
Labarai

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

10 hours ago
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
Manyan Labarai

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

12 hours ago
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina
Labarai

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

13 hours ago
Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara
Manyan Labarai

Matasa Sun Ƙona Ofishin NDLEA, Sun Kutsa Fadar Sarki A Kwara

14 hours ago
Next Post
Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Farfadowar Darajar Naira, Tsadar Kaya Na Ci Gaba Da Lulawa Sama

Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149

July 1, 2025
Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

July 1, 2025
Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

June 30, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.