Tsohon Ministan kula da harkokin Niger Delta, Senator Godswill Akpabio, ya janye takarar neman tikitin Shugaban Kasa ga Bola Tinubu domin ya zama Shugaban Kasa a Nan gaba.
Ya sanar da hakan ne a lokacin da ke jawabi Kai tsaye a wajen taron APC da ke gudana a Abuja yanzu haka.
Tsohon ministan ya kuma bukaci magoya bayansa da daliget da su zabi Tinubu domin imanin da ya yi na cewa zai iya Kai Nijeriya tundun mun tsira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp