Kwanaki kadan bayan tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe Tikitin takarar Shugaban kasa a zaben fidda gwani a Jam’iyyar PDP, wata kungiyar ‘ya’yan jam’iyyar APC a yankin Neja-Delta, sun koka kan yadda aka yi wa Jam’iyyar zagon kasa a yankin ta yin amfani da hukumar kula da Yankin (NDDC).
A cikin wata wasika da kungiyar mai kishin APC a yankin Neja-Delta ta aika wa shugaba Buhari da shugabannin jam’iyyar APC ta kasa, wacce wasikar ta samu sa hannun Ebibomo Akpoebide da Menegbo Nwinuamene da Itam Edem, ta yi gargadin cewa “Babu yadda APC za ta iya cin zabe a yankin Neja-Delta” sai dai in an gyara kura-kurai a NDDC kuma an kaddamar da hukumar NDDC bisa ga dokar da ta kafa Hukumar.
A cewar kungiyar, “Cif Akpabio tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom sau biyu kuma Sanata har zuwa 2018 a karkashin jam’iyyar PDP, ya zo jam’iyyar APC ne don ruguza jam’iyyar. Ya mayar da jam’iyyar koma baya ta fuskoki da dama amma muna fatan da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki za mu iya dawo da martabarta kafin babban zabe mai zuwa. ”
Da yake kira ga shugaba Buhari da shugabannin jam’iyyar APC da su gyara matsalolin da Cif Akpabio ya aikata tare da gyara barnar da jam’iyyar APC ta yi a yankin, ya kara da cewa “a halin da ake ciki, APC ba za ta iya cin zabe a yankin ba har sai an gyara wadannan kura-kuran.