Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ba za ta kidaya kuri’un rumfunan zaben da aka samu tashin hankali a zaben gwamnan jihar Bayelsa da za a yi a ranar Asabar ba.
Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a Yenagoa, a wani taron masu ruwa da tsaki.
- An Kwace Kambun Hilda Baci A Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
- Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Yajin Aikin Da Za Mu Shiga – NLC
Yakubu wanda Kwamishinan INEC na kasa mai sa ido a Akwa-Ibom, Bayelsa da Ribas, Misis May Agbamuche-Mbu ta wakilta, ta ce INEC za ta tura BIVAS a duk rumfunan zabe domin gudanar da zabe.
“Ina so na sanar da ku cewa BIVAS dinmu an kera su ne sabora INEC, don haka bayanan INEC da sunan jam’iyyu suna kan BIVAS, don haka duk BIVAS da kuka gani babu bayanan INEC ba ta INEC ba ce.
“Wani abu kuma, muna da dukkan jerin lambobin BIVAS da za mu yi amfani da su, za a sanya takardar sakamakon zabe a rumfunan zabe.
“A duk inda aka samu tashin hankali ba zai za mu lissafa kuri’un wurin ba.
“Mun horar da dukkanin ma’aikatan wucin gadi da za a tura wuraren zabe, an raba kayan zabe ga dukkanin ofisoshin kananan hukumomi takwas na jihar, ana ci gaba da wayar da kan masu kada kuri’a,” in ji shi.
Yakubu ya kara da cewa: “Mun shirya jigilar ma’aikata da kayan aiki domin tabbatar da cewa an bude rumfunan zabe a kan lokaci.
“Domin ingantacciyar kulawar wannan tsari, mun tura kwamishinonin kasa guda biyu, da kwamishinonin zabe guda takwas don tallafa wa ofishinmu da ke Bayelsa, ina mai tabbatar muku da kudurinmu na tabbatar da zabe mai inganci a ranar Asabar.”
Da yake jawabi, kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Tolani Alausa, ya ce ‘yansanda sun shirya tsaf domin tabbatar da zaben da za a yi a ranar Asabar cikin kwanciyar hankali.