Wata kungiya mai goyon bayan mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ta yi kira ga wakilai (Deliget) da su zabi Osinbajo a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a babban taron zaben fidda gwani a jam’iyyar da za a yi tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga watan Yuni 2022 a Abuja.
Ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai dauke da sa hannun Liberty Olawale Badmus a madadin kungiyar OSM, ta ce bisa la’akari da nasarori da gogewa da ya samu, Farfesa Osinbajo ne ya fi dacewa ya jagoranci Nijeriya daga 2023.
Sanarwar na cewa, “Yana da Matukar muhimmanci da farko mu fahimci tarihin inda muka fito da kuma inda muke so muje nan gaba kadan, wato gina kasar da muke buri kuma ta zama alfaharinmu, kuma musani wannan itace kasar mu Wacce aka samar damu acikinta. Ba mu da Wacce ta fita. Muna fatan mu zama masu kishin kasa, hadin kai, soyayya da zaman lafiya da adalci ga kowa.
“muna fatan kasa wacce za mu Kira kan mu ‘yan Nijeriya gaba daya ba wai ‘yan wata kabila ba.
“Irin Wannan sake daidaitawa al’amuran al’ummarmu yana farawa ne daga wakilanmu (Deliget) masu daraja wajen Zaben Shugaba Wanda ya cancanta da Jagorantar al’umma”.