ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Ghana: Sojin Kasar Sun Yi Damarar Samar Da Zaman Lafiya

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Ghana

Babban Hafsan Sojin Kasar Ghana, Manjo Janar Bismarck Kwasi Onwona, ya gargadi sojojin kasar da su kaucewa yaudarar ‘yan siyasa kana kar su karkata ta wani bangare siyasa gabanin babban zabe na watan Disamban shekarar 2024.

Ya kuma jaddada bukatar jami’an soji su nuna kwarewa ba tare da shiga harkokin siyasa ba a daidai lokacin da kasar ke tunkarar wannan lokacin mai muhimmanci.

  • Yadda Ake Kosan Filantan
  • Rungumar Harkar Noma Mafita Ce Ga Ma’aikata Masu Ritaya

Da yake jawabi a kan rawar da sojojin ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a lokacin zaben, Manjo Janar Onwona ya jaddada aniyar rundunar sojin ta ci gaba da tabbatar da kwarewa.

ADVERTISEMENT

Ya yi kira ga daukacin jami’an soja da su mai da hankali kan ayyukansu domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, yana mai tabbatar wa ‘yan kasar Ghana a shirye sojojin suke wajen kare kasar a lokacin zabe.

A jawabinsa, Manjo Janar Onwona ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da su yi aiki yadda ya kamata, inda ya bukace su da su guji yada labaran karya da na kirkira.

LABARAI MASU NASABA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

Ya kuma yi gargadin cewa bada rahotanni marasa tushe na iya yin barazana ga zaman lafiyar kasar da ta da fitina, musamman a lokacin zabe mai matukar muhimmanci.

“Ban ware wani rukuni na mutane ba. Abin da nake nufi shi ne, kada wani ya yaudare su; kama daga ‘yan siyasa, ‘yan jarida, ko kuma ‘yan kasuwa”.

“Mu ba ‘yan siyasa ba ne, aikinmu shi ne kare Kundin Tsarin Mulki. Don haka, ina magana ne ga kowa da kowa da ke da niyyar yaudarar kowane jami’in Sojojin ta hanyar da ba ta dace ba, ”in ji shi.

Shugaban rundunar sojin ya yi wannan jawabi ne a lokacin kaddamar da wani sabon wurin kwana ga jami’an da ke babban ofishin rundunar da ke Kumasi.

An gudanar da aikin ne da nufin inganta rayuwar jami’an soji, wanda ke karkashin kulawar Birgediya Janar Michael Kwadwo Opoku, babban kwamandan runduna ta tsakiya.

Ana sa ran sabon ginin da aka kaddamar zai inganta jin dadin jami’an soji da ke yankin, a daidai lokacin da rundunar ke shirin tallafawa kokarin kasar na gudanar da zabe cikin nasara da lumana a cikin watan Disamba.

A wani labarin kuma, Amurka za ta hana wasu ‘yan ghana biza. Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disambar 2024.

Amurka ta sanar da wani tsarin takaita biza ga mutanen da hukumomin Washington ke ganin suna da alhakin haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya a Ghana, gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a watan Disamba a kasar wacce ke Yammacin Afirka.

“Wannan tsarin takaita biza zai shafi wasu mutanen da ke cin dunduniyar tsarin dimokradiyya ne kawai kuma ba ana nufin za ta shafi al’ummar Ghana ba ko kuma gwamnatin Ghana,” in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Litinin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai
Kasashen Ketare

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

December 14, 2025
Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni
Kasashen Ketare

Trump Ya Caccaki Kasashen Turai Bayan Ayyana Nahiyar A Matsayin Mai Rauni

December 14, 2025
Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo
Kasashen Ketare

Rwanda Ta Musanta Hannu A Rikicin Da Ya Barke A Kibu Da DR Congo

December 14, 2025
Next Post
Ɗaliban Cyprus: Zamfara Ta Samar Wa Ɗalibanta ‘Yanci Da Ke Karatu A Gida Da Ƙetare

Ɗaliban Cyprus: Zamfara Ta Samar Wa Ɗalibanta 'Yanci Da Ke Karatu A Gida Da Ƙetare

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.