Gabanin zaben gwamnan Jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyun siyasar da za su fafata a zaben za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 8 ga watan Nuwamba a Akure, babban birnin jihar.
Yarjejeniyar zaman lafiya da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) da INEC suka shirya, wani bangare ne na kokarin ganin an gudanar da zaben cikin lumana.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro da kungiyoyin farar hula.
- Kurar Da Ta Biyo Bayan Gurfanar Da Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
- Zargin Cin Zarafin Likita: Gwamna Yusuf Ya Roki Likitoci Su Bayar Da Kofar Sulhu
Yakubu ya kara da cewa INEC za ta gudanar da tantancewar karshe na shirye-shiryenta a mako mai zuwa, wanda zai hada da masu ruwa da tsaki, jami’ai, hukumomin tsaro, da masu samar da sufuri. Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta gano wasu guraren da za a iya ta da zaune tsaye a Jihar Ondo tare da sanar da jami’an tsaro don samar da ingantaccen tsaro da matakan kariya.
Dangane da shirin masu kada kuri’a kuwa, Yakubu ya ruwaito cewa daga cikin katinan zabe guda 89,777 da aka raba wa Jihar Ondo, guda 64,273 ne aka amsa, wanda ya nuna an samu kashi 71.6 cikin dari. Ya kara da cewa, nan ba da dadewa ba za a sanya alkaluman tattara bayanai na katin zabe na kowanne daga cikin rumfunan zabe 3,933 a fadin jihar a shafin hukumar INEC, inda za a tabbatar da gaskiya wajen gudanar da sakamakon zaben.
Yakubu ya kuma yi karin haske kan ci gaban da aka samu a harkar zabe da suka hada da tantance masu kada kuri’a, shigar da sakamakon zabe zuwa na’urar INEC ta hanyar duba sakamakon zabe (IReV), da kuma amincewa da masu sa ido da kuma manema labarai.