Jam’iyyar PDP a jihar Osun ta zargi jam’iyyar APC mai mulki a jihar bisa son yin amfani da ‘yan bangar siyasa domin lashe zaben gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Julin 2022.
PDP ta bukaci Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Julius Alawari Okoro da kuma DIG Johnson Babatunde Kokum, da su gaggauta dakile aukuwar yunkurin na APC.
- Gwamnatin Tarayya Ba Ta Muhimmanta Tsaro Ba – Matawalle
- Gwamnatin Buhari Za Ta Yi Mai Yiwuwa Wajen Tabbatar Da Tsaro A Kasar Nan – Malami
PDP ta kara da cewa bisa bayanan da ta samu, ta na kuma zargin APC da yunkurin shigo da mutane dauke da malamai domin ta tayar da hargitsi a lokacin zaben.
Shugaban kwanitin riko na PDP a jihar, Akindele Adekunle ne, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jihar, inda ya yi zargin cewa APC za ta shigo da ‘yan bangar siyasar ne daga jihar Legas wadanda kuma za a kama wa dakuna a otal-otal.
A cewar Adekunle, “Muna da bayanan APC ta tura irin wadandan ‘yan bangar siyasar zuwa shiyoyin jihar har da a shiyyar Iwo inda aka kashe jami’in PDP.
Sai dai, a martanin da kakakin yakin neman zaben gwamnan APC, Sunday Akere, ya mayar ga PDP ya ce, zargin na PDP abin dariya ne domin PDP ta riga ta hango ba za ta samu nasara a zaben ba.
Ya kara da da cewa, tuni an san APC jam’iyya ce da ba ta goyon bayan dukkan nau’in tayar da rikici.
A karshe, ya yi kira ga daukacin ‘yan jihar da suka kai munzalin jefa kuri’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin su sake zabar gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola don yin tazarce a karo na biyu.