Dantakarar gwaman na jam’iyyar PDP a jihar Fulato a zaben da aka kammala, Sanata Jeremiah T. Useni, ya bayyana dalilin shin a kin amincewa da sakamakon zaben gwamana, wanda Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewar suna da wasu shedun da zai gabatar akan magudin da aka tafka.
Hukumar zabe amakon daya wuce ne ta bayyana gwamna Simon Bako Lalong na jam’iyyar (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan data bayyana yadda shi wancan zaben wanda bai kammala ba, wanda kuma hakan ce ta sa aka sake yin shi zaben raba gardama.
Amma kuma Useni ya bayyana cewar a wani taron manema labarai cewar jam’iyyar shi ta PDP da kuma shi kan shi, cewar sun yi nazarin sakamakon zaben kuma daga karshe suka ga shi abin bai gamsar dasu ba.
“Tawaga ta da kuma ni sun duba shi sakamakon wanda aka bayyana, wanda Hukumar zabe ta bayyana, da kuma wasu takardun bayanan da aka ba ma’aikatan mu, bayan nan kuma muna da namu kwararan dalilan , cewar ba ayi mana adalci ba, a wannan zaben saboda yadda aka tafaka magudi mai yawa.
“Bayan dana tuntubi mutane, sai naga bai dace ban a amince da shi sakamakon zaben bamu yarda dashi ba, saboda an yi mana rashin ba, don haka sai muka fada ma lauyoyin mu, su yiu dukkan abubuwan da suka kamata, saboda a amso mana kujerar da aka yi mana fashi .
“Zamu yi dukkan abubuwan da suuka dace saboda mu dawo da darajar jihar Fulato kamar yadda take shekaraun da suka na baya.