Shugaban Jam’iyyar PDP mai adawa na kasa, Dakta Iyorchia Ayu ya sanar da cewa, sakamakon zaben kujerar Gwamna na jihar Osun ya nuna cewa, al’ummar jihar sun yunkro.
Ayu a cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi ya yi nuni da cewa, kamar yadda zaben na Osun ya nuna, haka ‘yan Nijeriya za su kara yunkuro wa a zaben 2023 ta hanyar zabar dan takarar shugaban kasa na PDP Alh. Atiku Abubakar.
Ya yi zargin cewa, babu irin shige da ficen da Gwamnan jihar mai ci Oyetola da APC basu yi ba don su hana PDP lashe zaben, inda ya kara da cewa, Oyetola ya hana PDP gurin da za ta yi babban gangamin yakin neman kujerar ta gwamna a jihar.
Ya kara da cewa, a ranar 26 ga watan Nuwambar 2010, an yiwa PDP murdiya a jihar Osun, inda ya bayyana cewa, shekaru hudu da suka wuce Sanata Adeleke a PDP ya lashe zaben kujerar gwamna jihar, amma APC ta murde zaben.
A cewarsa, yau gaskiya ta yi halinta ganin cewa, PDP a jihar ta samu nasara, inda ya kuma taya Adeleke da al’ummar jihar murnar lashe zaben.
Ayu ya sanar da cewa, lashe zaben na PDP ‘yar manuniya ce ga irin mulkin kama karya na APC a jihar.