ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Matsalar Tsaron Nijeriya (Ra’ayinmu)

by Sulaiman
4 years ago
Nijeriya

Ba Nijeriya kadai ke fuskantar matsalar tsaro ba, kasashe da dama na fuskantar irin nasu matsalar.

Amma yadda kasashen ke tunkarar lamarin yayin da matsalar ta addabe su shi ne abin dubawa. Daga dukkan alamu sauran kasshen duniya sun samar wa kansu hanyoyin magance matsalar tsaro, amma lamarin tabarbarewar tsaro ya zama tamkar a Nijeriya kadai ake fuskantar ta, don a halin yanzu lamarin ya fara zama jiki a kasarmu, kullum ka tashi zaka ji sabon labari, kuma har yanzu babu wani mataki na gaggawa da ake dauka don kawo karshen lamarin.

  • An Kashe Mutane Biyar, Fursunoni 879 Sun Tsere A Harin Gidan Yarin Kuje – Gwamnati

Al’umma sun gaji da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa, matsaloli irin su kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci sun zama ruwan dare, lamarin ma ya kara ta’azzara ne da karuwar wasu laifuffukan kamar su safarar muggan kwayoyi, sace sace ta intanet da kuma safarar sassan biladam.

ADVERTISEMENT

Babbar matsalar tsaro a Nijeriya shi ne yadda jami’an tsaronmu ke amfani da tsofaffin hanyoyi wajen yaki da ‘yan ta’adda, ‘yan ta’addan da suke amfani da kayan aiki na zamani wajen gallaza wa al’umma.

Masana sun bayyana cewa, rashin kayan aiki na zamani ne daliin da yasa gwamnati da hukumominta suka kasa yin komai, abin duk ya fi karfinsu, basa iya yin takabus wajen kare al’ummar jihohi irinsu Borno, Zamfara, Katsina, Kaduna, Nija da Nasarawa da kuma yankunan Kudu masu Gabas.

LABARAI MASU NASABA

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

Babu tantama wasu jihohi a kasar nan na fuskantar mamaya daga ‘yan ta’adda akwai kuma bukatar kai musu daukin gaggawa don tabbatar da ceto rayuwar al’ummar yankunan.

Wasu daga cikin manyan dalilan da aka gano suna kara wutan ayyukan ta’addanci a kasar nan sun hada da rashin aikin yi a tsakanin matasa da tsananin talauci a tsakanin al’umma. Wadanan sune suka fi bukatar a gaggauata kai musu dauki, yakamata a basu daukin daya wuce yadda ake basu a halin yanzu.

A ra’ayimu a kwai bukatar samar da ayyukan yi ga matasa da kuma samar da yanayin da harkokin kasuwanci za su bunkasa ba tare da wasu cikas ba, bai kamata a ce, kasa kamar Nijeriya da ke tattare da dinbin albarkatun kasa da yawan al’umma amma kuma ta kasance hedikwatar talauci na duniya ba.

A ra’ayin wannan jaridar, cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar tsaro a fadin tarayyar kasar nan. Masu rike da mafun iko suna cigaba da babakere tare da azurta kansu ta hanyar amfani da kudaden gwamnati, sun yi watsi da kula da hakkokin al’umma wanda shi ne aikin da suka rantse za su kare.

Ayyuka kuma sun yi wa jami’an tsaromu yawa kuma gashi ba a basu albashin da yakamata a kan haka basu sa kishin kasa a gudanar da aiki su, a kan haka matsalar ke cigaba da barazanar hadiye al’umma gaba daya.

Daya daga cikin manyan tambayoyin da ke bukatar amsa anan shi ne, ta yaya bamabamai da manyan bidigogi na zamani suka shigo kasar nan suka kuma fada hannun ‘yan ta’adda?, a halin yanu dai an dora wannan laifin a kan yadda iyakokin kasar suke tamkar a bude babu cikakken tsaro, wanda hakan yake sa bakin haure suke samun saukin shigowa daga kasashe makota kamar su Nijar, Jamhoriyar Benin da Chadi sau da yawa kuma dasu ake amfani wajen aikata muggan laifukka a sasan kasar nan.

Rashin samar da cigaba a sassan yankuna kasar nan shi ma ya taimaka wajen haifar da matsalar tsaron da muke fuskanta, musamman ganin yadda wasu kabilu da al’ummu ke korafin ana barinsu a baya wajen samar da ababen more rayuwa.

Irin wannan ke haifar da rashin jin dadi a tsakanin mutane, abin da kuma yake kai ga tayar da hankula da aikata ayyukan ta’addanci da kuma nuna halin ko-in-kula, wanda ta hakan suke fatan gwamnati za ta kula dasu ta san da zaman su.

Tabbas kare rayuwa da dukiyar al’umma shi ne muhimmin aikin gwamnati, ya kuma kamta gwamnati ta dauke shi da matukar muhimmanci, tunda wannan aiki yana nan a cikin kudin tsarin mulkin kasar nan a sashi na 14 (2) (b) na dokokin 1999 Nijeriya (kamar yadda aka gyara), na tabbatar da tsaro da hakkokin raywaur al’umma to ya zama dole gwamnati ta dauki lamarin da matukar muhimmanci, bai kamata jami’an gwamnati su kauce daga wanan hakkin da ke kansu ba, musamman ganin a halin yanzu ana neman daukar ayyukan ta’addanci tamkar wata harkar kasuwanci, maimako a fuskanci yaki da ‘yan ta’addan sai aka bige da jefa wa juna laifukka.

Abin akwai takaici ta yadda mahukunta suka kasa kai hari tare da kama masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar nan, yakamata ace an kama su an kuma gurfanar dasu a gaban shari’a don su dandana sakamakon ayyukansu.

A ra’ayinmu, wannan halin da ake ci, ya cancanci a sake duba bukatar samar da ‘yansanda yankuna, muna kara kira ga gwamnati da ta duba wannan bukata. Samar da ‘yansandan yankuna zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta a fadin tarayyar kasar nan.

Ya kuma kamata a samar da kudade don sayen kayan aiki na zamani ga jami’an tsaron, a kuma samar da hanyoyin gano shirin aikata ta’addanci tun kafin a aiwatar dashi, ta yadda za a iya dakike aikatawa.

Muna kuma kira ga a kan bukatar samar da yanayin tafiya da kowa da kowa a yaki da ta’addanci, dole gwamnati, jami’an tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu, Malaman addini, sarakunan gargajiya su daukar wa kansu aiki yaki da ta’addanci.

Munada bukatar hadin kan kowa da kowa a wajen kawo karshen wannan matsalar kafin ta hadiye mu gaba daya.

Nijeriya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada
  • Sulaiman
    Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

Ko Yakin Iran Zai Kawo Karshen Kawancen Amurka Da Kasashen Larabawa?

May 17, 2026
Nijeriya
Rahotonni

Yadda Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Ta Sauya Fasalin Majalisar Dokokin Kasa

May 16, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Rahotonni

Almajiranci:Matsala Ko Maslaha

May 10, 2026
Next Post
Atiku Abubakar, Saraki, Tambuwal Da Bala Kaura Sun Taya Adeleke Murnar Lashe Zaɓen Osun

Atiku Abubakar, Saraki, Tambuwal Da Bala Kaura Sun Taya Adeleke Murnar Lashe Zaɓen Osun

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.