Kura ta turnike sakamakon zaben da aka gudanar a kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna biyo bayan cece-kuce saboda ba a samu kayan zabe da jami’an zabe a mafi yawan wuraren da aka ce an yi zaben.
Sai dai masu kada kuri’a sun fito a wasu cibiyoyin zabe amma ba su sami daman kada kur’ansu ba sakamakon yadda malaman zaben suka iso a makare.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Me Najeriya Za Ta Iya Samu Daga Tsarin BRICS?
A rumfar zabe ta Gwamna Uba Sani da ke Kawo Kaduna ta Arewa an samu fitowar masu kada kuri’a da dama, amma akwati daya tilo da aka yi zargin cewa babu takardar sakamakon zaben, lamarin da ya kai ga zanga-zangar da ta kawo cikas ga sakamakon zaben.
A makarantar firamare da gwamnan ya kada kuri’a, akwai rumfunan zabe guda uku, amma akwati zabe guda daya tilo aka samu matsala, lamarin da ya haifar da tashin hankali, inda aka tattaro motocin Hilud sama da 20 dauke da jami’an tsaro zuwa wurin domin kwantar da taroma, wanda mutane suka dage cewa dole ne a samar da takardar sakamako zabe kamar yadda wasu daga cikinsu ke rera wakar “PDP muke so”.
Saboda tashin hankalin da aka yi, gwamnan ya kasa zuwa wurin da za a gudanar da zaben, sai da aka tara jami’an tsaro da yawa a wurin, sannan ya samu damar kada kuri’a bayan karfe 4 na yamma lokacin da ake sa ran kammala zaben.
Wasu rumfunan zabe sun samu kayan zabe ne bayan ya wuce lokacin kada kuri’a.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Edward Masha, ya yi zargin an tabka magudi a zaben.
Masha, yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida, ya nuna damuwa game da bacewar muhimman kayan, musamman takardun sakamakon.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP za ta kalubalanci lamarin a kotu, sannan kuma za ta ci gaba da nema wa mutane adalci. Masha ya bayyana wasu kura-kurai da tashin hankali da aka samu a lokacin zaben.
Masha ya bukaci masoya dimokuradiyya da hukumomin tsaro da su lura da lamarin, inda ya ce, “Jihar Kaduna ba tana cikin rashin lafiya, kuma dimokuradiyya ta tafi. Muna bukatar mu jawo hankalin jama’a tare da neman adalci.”
Shugaban na PDP ya bukaci ‘yan jam’iyyar da magoya bayansa da ka da su karaya. “Za mu ci gaba da fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da adalci. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba,” in ji shi.
Tun da farko dai, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM), ta ce jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 da na kansiloli 255.
Da take bayyana sakamakon zaben, shugabar hukumar, Hajara Mohammed, ta ce jam’iyyun siyasa takwas ne suka shiga zaben, inda APC ta lashe kujerun shugabanni kananan hukumomi 23 da kansiloli 255.
Ta kara da cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi nasara a Birnin-Gwari, Chikun, Igabi, Ikara, Jaba, Jema’a, Kachia, Kaduna ta Arewa, da Kaduna ta Kudu.
Sauran kananan hukumomin da jam’iyyar APC ta lashe a cewar shugabar sun hada da Kagarko, Kajuru, Kaura, Kuaru, Kubau, Kudan, Lere, Makarfi, Sabon Gari, Sanga, Soba, Zango-Kataf da Zariya.
A cewar shugabar SEICOM, ADC, APC, APGA, LP, NNPP, PDP, PRP da YPP ne suka gabatar da ‘yan takararsu a zaben.
Sai dai mutane da dama sun nuna rashin gamsuwarsu kan yadda zaben ya gudana, musamma ma jam’iyyun adawa wanda suka bayyana cewa karfa-karfa kawai aka yi amma ba zabe ba.