Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, ta bayyana cewar za a yi wa ‘yan takara gwajin miyagun kwayoyi kafin ba su damar tsayawa takara.
Shugaban hukumar zaben jihar, Farfesa Sani Malunfashi ne, ya shaida wa manema labarai a Kano.
Ya bayyana cewar hukumar za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024.
Hukumar zaben ta kuma sanar da cewa haramun ne manna fastocin yakin neman zabe a ginin gwamnati, fada, da wuraren ibada, kuma za ta hana duk wanda ya keta wannan doka tsayawa takara.
Ana sa ran gudanar da zaben ne a kananan hukumomin jihar 44.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp