Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC), ta ce za ta gudanar da gwajin shan miyagun kwayoyi a kan dukkanin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi da kansiloli da za su shiga zabe.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne, ya bayyana wannan lokacin da ya ziyarci hedikwatar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), a Kano ranar Talata.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Budewar Dandalin Mata Na SCO
- Gwamnatin Borno Ta Kafa Sansanin Kula Da Wadanda Ambaliya Ta Shafa
Farfesa Malumfashi, ya bayyana cewa KANSIEC za ta duba dukkanin ‘yan takarar da ke neman shugabancin kananan hukumomi da kansiloli don tabbatar da cewa ba su yi amfani da kwayoyi ba.
Ya roki NDLEA ta taimaka wajen gudanar da gwajin kuma ta aike da sakamakon ga KANSIEC, wanda za su yi amfani da shi wajen tantance cancantar ‘yan takarar.
Ya tabbatar da cewa hukumar zaben a jihar tana da niyyar hana wadanda ke amfani da kwayoyi samun iko a kananan hukumomi.
Ya kuma yi gargadi cewa zaben wadanda ke amfani da kwayoyi a shugabancin kananan hukumomi zai kara tabarbarewar matsalar ta’ammali da kwayoyi da kuma iya jefa kananan hukumomi cikin talauci ta hanyar ta’azzara amfani da miyagun kwayoyi da aikata laifuka masu alaka da kwayoyi.
Farfesa Malumfashi, ya kuma nemi goyon bayan NDLEA wajen tabbatar da tsaro yayin zabe da bayan zabe.
A martaninsa, Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, ya tabbatar wa shugaban hukumar cewa rundunarsa a shirye ta ke ta bayar da dukkanin goyon baya da hadin kai don gudanar da zabe ba tare da matsala ba a jihar.
A cikin bayanin da Bashir Habib Yahaya, Daraktan Wayar da Kan Jama’a na KANSIEC, ya yi, ya bayyana cewa taron ya hada da gabatar da ka’idojin zabe da jadawalin zabe ga NDLEA, domin sanin ta inda za ta bayar da gudunmawa.