A yayin da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a Jihar Kano ke kara karatowa, ‘yan takara sai karuwa suke yi, musamman ma a jam’iyya mai mulki ta NNPP, wanda yanzu haka akwai masu shawa’ar shugabancin kananan hukumomin 44 da suka haura mutum 400, inda kusan kowacce karamar hukuma ke da akallah masu zawarcin kujerar sama da mutum 20.
Wannan ambaliyar ‘yan takara a karkashin tutar jam’iyya mai mulki baya rasa nasa ba da irin salon jagoran darikar Kwankwasiyya, Rabiu Masu Kwankwaso wanda a baya a lokacin mulkinsa ya bayyana cewa, ‘kazarsa ta yi kwai 44 kuma ba za ta yi baragurbi ba’, hakan ta sa wasu ke ganin irin wannan za a maimaita a kakar zaben mai zuwa.
- Laifukan Zabe Barazana Ne Ga Samun Sahihan Zabuka A Nijeriya – INEC
- Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Wata Mata Da ‘Ya’yanta Biyu Bayan Ruftawar Gini A Kano
Sai dai kuma a wannan karo ana ganin kila a fuskanci turjiya, domin tun yanzu an fara jin bullar wasu ‘yan takara da ake kira da ‘yan takarar Miller da kuma wasu da ake wa lakabi da Abba tsaya da kafarka.
Wannan kuma baya rasa nasaba da irin dabaibayin da jagoran Kwankwasiyyar ya yi wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf. Wadda wasu ke ganin gwamnan ba shi da wani katabus kan abin da ya shafi tsayar da ‘yan takara, domin hakan ta faru a baya a lokacin nada kantomin riko, wanda Gwamna Abba na kasar Saudiyya aka yi kuma aka gama.
Wata majiya ta tsegunta wa Jaridar LEADERSHIP HAUSA cewa, ana zargin ware wasu mutane uku da ake ganin su ne za su yi uwa kuma su yi makarbiya wajen tsayar da dukkanin ‘yan takara, musamman a wuraren da aka kasa samun maslaha.
Haka kuma batun maslahar ma ana ginin maslaha ce ko a sa a baka. Domin an fara jin wasu na fara tanadar kudin na gani ina so domin mika wa masu ido da kwalli.
Amma kuma dole sai jam’iyyar NNPP ta yi karatun ta nutsu, domin jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar APC da takwararta ta PDP na ganin sahun gwamanti mai mulki a Kano ya shiga rafkanuwa, musamman idan aka yi la’akari da badakalar kudade da ke kara bayyana wadda ake zargin wasu na kusa da gwamnati da hannu a ciki dumu-dumu.
Wadannan matsaloli da su ne jam’iyyun adawa za su matsa a lokacin yakin neman zabe, sai kuma batun masarautu da aka mayar da sarakuna masu daraja ta biyu a birnin na Kano, ita ma wannan matsala za ta yi tasiri, musamman a yankunan da suka fara amfanar sabbin masarautun wadanda bayan shigowar gwamnati NNPP ta rushe su tare da mayar da su masu daraja ta biyu, wanda hakan ya yi matukar fusata mazauna wadannan yankuna.
Haka ma batun kudaden tsayawa takara da hukumar zabe mai zaman kanta a Kano ta ayyana, na nuni da wani shiri na hana duk wani mai karamin karfi ko wadanda ba su da gwamnati samun damar shiga takarar a dama da su sakamakon tsawwala kudaden takarar, inda aka a je naira miliyon 10 a matsayin kudin na gani ina so ga duk mai bukatar tsayawa takarar kujerar shugabancin karamar hukuma zai biya, yayin da kansila kuma zai biya naira miliyon 5 lakadan.
Wasu na ganin jam’iyyar NNPP za ta yi amfani da karfin ikon da ke hannunta wajen saya wa duk wadanda suka tsayar takara fom, yayin da sauran jam’yyun da ba su da mulki ana ganin an takura musu.
Wannan ta sa yanzu haka wasu gamayyar kungiyoyi ke shirin gurfanar da hukumar zaben mai zaman kanta ta Jihar Kano a gaban kotu domin bin ba’asin tsawwala kudazen takarar.
Koma dai me ake ciki ‘yan makonni kadan suka rage domin gudanar da zaben fid da gwani, wanda sakamakonsa ne zai nuna wa saura jam’iyyun makomarsu da kuma ‘yan takara da ba su da uwa a gindin murhun jam’iyya mai mulki, wanda ake kyautata zaton za a yi bari wanda jam’iyyun adawa za su daka wasoson su.