Wata babban kotun tarayya da ke zamanta a Osogbo, babbar birnin Jihar Osun, ta rushe zabukan kananan hukumomin jihar da hukumar zaben jihar (OSIEC), ta gudanar a kwanakin baya.
Da ya ke yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Ayo-Nathaniel Emmanuel, ya ayyana zabukan kananan hukumomin da OSIEC ta gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Oktoban 2022 a matsayin haramtacce da ke cike da kura-kurai bisa gudanar da shi ba tare da bin dokar zabe ta 2022 ba.
- Taiwan Bangare Ne Da Ba Za A Iya Raba Shi Da Kasar Sin Ba
- Al-Mustapha Ya Yi Tonon Silili Kan Shigo Da Makamai Gabanin Zaben 2023
Sannan, kotun ta umarci wadanda aka ce an zaba da su gaggauta ficewa daga sakatariyar kananan hukumomin da ofis-ofis, yayin da ta umarci a sake gudanar da sabon zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli.
Jam’iyyar PDP ce dai ta garzaya kotun inda take rokon kotun da ta dakatar da OSIEC daga ci gaba da tsare-tsaren zaben.
Kodayake, reshen jam’iyyar PDP ta jihar sun yi lale da murna gami da annashuwa bisa wannan hukuncin, sun ce jam’iyyar ta tsaya Kai da fata wajen tutsu ga kokarin Gwamnatin Gwamna Gboyega Oyetola mai barin gado na gudanar da lamura ba bisa ka’ida ba.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan hukuncin, mai rikon shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Dakta Akindele Adekunle, ya ce, sama da naira biliyan 1.5 da gwamantin Oyetola ta kashe wajen kan walwa da jin dadin ma’aikatan da suka gudanar da zaben Kananan Hukumomin a matsayin kudaden da aka yi asararsu a banza, kari a kan wasu miliyoyi da aka kashe ba bisa ka’ida ba wajen biyan albashi da alawus-alawus na mutanen da ya kira ‘shugabannin kananan hukumomi na bogi’
“Ai tun da farko mun yi gargadin kar a gudanar da dauki dora (selection) na bogi da sunan zabe. Mun bi dukkanin matakan shari’a wajen ganin an hana OSIEC take tsarin demokradiyya. Shugaban hukumar ma da kansa Lauya ne amma ya amince wajen gudanar da abubuwan da suka saba wa doka.
“Wannan hukuncin na nuni da matakan gyara kura-kuran da aka tafka. Kuma fa da gangan gwamnan da ke shirin barin gado ya aikata hakan. Za mu cigaba da bin dukkanin matakan shari’a wajen kare hakkokin al’umman jihar”.