Magoya bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun yi arangama da ‘yansanda a jihar bayan barkewar zanga-zanga kan hukuncin kotun daukaka kara.
‘Yansandan sun tarwatsa magoya bayan gwamnan a yankin Dan Agundi da ke babban birnin jihar, wadanda suka fito domin gudanar da addu’o’i na musamman kan yadda kalubalantar hukuncin kotun.
- Zaben Kano: Abba Ya Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli
- Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Kansiloli 8, Ta Karɓe Ragamar Majalisar Kagarko
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano da ta tsige Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP, tare da ayyana dan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.
Zanga-zangar na zuwa ne ya biyo bayan fitar kwafin kundin hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da zaben gwamna Yusuf sabanin yadda kotun daukaka kara ta bayyana.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce a shirye suke su mutu domin neman a yi musu adalci.
Rundunar ‘yansandan Jihar Kano sun sha alwashin dakile duk wata zanga-zanga a jihar biyo bayan hukuncin da aka yanke kan kujerar gwamnan.
A watan Maris din 2023 ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Abba na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, amma kotun sauraron kararrakin zabe a jihar ta tsige shi a watan Satumba.
Kazalika, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun kasan ta yanke.