Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 22 cikin 25 na kujerun shugabannin kananan hukumomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Neja, NSIEC ta shirya a ranar Alhamis.
Daraktan Ayyuka na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja, Kwamared Ibrahim Aliyu Tunganwawa, ne ya sanar da sakamakon zaben a Minna.
- Shirin Nijeriya Na Yaki Da Talauci A Duniya
- Wakilin Sin Ya Bukaci A Kara Kokarin Taimakawa Kasashen Afirka Yakar Ta’addanci
Ya bayyana cewa ana dakon sakamakon sauran kananan hukumomin uku, inda ya ce jam’iyyun siyasa 13 ne suka shiga zaben.
A cewarsa, “Saboda wasu matsalolin da aka fuskanta a lokacin gudanar da zaben kansilolin kananan hukumomi, NSIEC za ta sake gudanar da zabukan a unguwanni biyu na kananan hukumomin Rafi da Kontagora.
“Yankunan biyu sune na Kusherki da Tungan Kawo da aka shirya gudanarwa a wannan Lahadi”.
Daraktan ayyuka na NSIEC, ya bayyana zaben kansilolin kananan hukumomin da aka gudanar cikin lumana da kwanciyar hankali tare da haifar da kananan matsaloli a kananan hukumomi uku da ake dakon sakamakonsu wanda suka hada da Katcha Agwara da Borgu.