Kungiyar Gwamnonin kasar nan sun nuna damuwarsu a kan furucin Miinistan Shari’a kuma Atoni-Janar na kasa Abubakar MalamI kan maganar biyan bashin dala miliyan 418 da ake bin wasu ‘yan Kwangila da wasu masu aikin tuntuba na kudin Paris Club.
Kungiyar ta kuma yi mamakin kan yadda Malami ya dage wajen tura kudaden na Paris Club ga wasu daidaikun jama’a masu zaman kansu alhali gwamnonin sun karyata ikirarin na masu aikin tuntuba wanda a yanzu, maganar na a gaban kotu.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
Mai magana da yawun kungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo ne, ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabin na Channels.
Barkindo ya sanar da cewa, kamata ya yi a bar kotun ta yanke hukunci kan maganar wacce ta ke a gabanta.
A cewarsa, “Mun dogara ne a kan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da kuma tsimayi daga gun kotun don ta yanke hukunci a kan batun”.
Barkindo ya kara da cewa, kamata ya yi mutane su tambayi Malami kan mene ne ya sa yake gaggawar biyan kudaden ga wasu daidaikun mutane bayan alhali maganar na a gaban kotu.
Ya ce, “Muna fadar hakan ne domin Ikirarin ba gaskiya bane domin maganar na gaban kotu kuma ita ce, za ta yanke hukuncin”.
Kakakin ya ce, kamata ya yi Malami ya jira kotun ta yanke hukunci kan maganar, inda ya kara da cewa, gwamnonin ba su da wani ja kan biyan kudaden.
In ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 2022 ne a taron Majalisar kasa, ya umarci Ministar kudi Zainab Ahmed, da ta dakatar da shirin fara gudanar da zabtare kudaden na Paris Club dala miliyan 418 har idan kotu ta yanke hukunci kan maganar.