Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da wani sako da muka samu na wata baiwar Allah, wadda ta bukaci da a boye sunanta. Inda take so a yi magana a kan yadda wasu mazan ba sa iya taimakawa matansu ko da kuwa suna da shi, musamman idan sun san matan suna da wata sana’a ko kuma aiki, sai su dauke hannayensu daga dukkanin abubuwan mafi yawan gaske da ya zama hakkinsu ne sai su jibga wa matansu. Face su dauki iya ci da sha kawai matsayin shi ne ya zamar musu dole kuma wajibin a yadda suke gani. Sutura ma nata da na ‘ya’yanta sai dai ta yi wa kanta da sauran abubuwan bukata, ko da kuwa samun ta bai taka-kara-ya karya ba, haka kuma koda shi din ya kasance mawadacin gaske, wanda samunsa ya ninka nata sau ba adadi, koda a ce tana neman taimako sai dai ya sa ta ranta a wajensa ba dai ya ba ta ta yi amfanin da za ta yi da su ba.
Dalilin haka ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me za a ce a kan hakan? Me hakan zai iya haifarwa? Me yake janyo hakan? Laifin waye tsakanin miji da matar? Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Aysha D. Fulani, Daga Jihar Kano:
Hakika wannan matsala ai ta zama ruwan dare mussaman mazajen yanzu, wallahi imaninsu yai karanci a kan wannan al’amarin abun sai dai mu ce Allah ya gyara wannan al’amari. Hakika wannan zai iya haifar da matsanancin rashin tausayi a tsakanin iyaye da yaransu, abun nufi shi ne matukar a ka ce za a ci gaba da tafiya a kan wannan turba tofa maza da yawa za su tsinci talatarsa a laraba, domin kuwa in dai yaro zai taso ya ga uwa ita ce take daukar duk wata ragama ta rayuwarsa tofa, makomar uba tana cikin halin kila wa kala a goben yaron nan. Wallahi tsantsar son zuciya ne ya janyo hakan, domin kuwa kasan cewa kai ne wanda Allah ya umarta ma wannan yankin to ko dole kayi idan kuma ba kai ba Allah yana kallonka. Ita mace tanada wani abu wallahi muddin ka kau da idonka a kan abin hannunta to da kanta za ta dinga kusanto maka da abubuwanta ta hanyar kyautata maka, da iyalenka da ‘yan’uwanka. Lefin maza ne a gaskiya domin kuwa da zarar sun ga kina juya taro ta koma sisi tofah har wani haushi-haushi za a rika ji naki, baki da damar tambayan abu za a ce ina abun kaza da ki ke kiyi a ciki mana. Hanyar gyara na gun maza, wallahi ku ji tsoron Allah ku sani komai da ku ke yi Allah yana kallonku, idan kun kyautata, Allah zai kyautata muku. Mu ma mata mu ji tsoron Allah a kan dukkan wani al’amari na gida idan an mana mu gode tare da yin addu’a, idan mun nema abun ya yi albarka mu taimaka ma mazajenmu domin ita kyautatawa na da matukar dadi. Ma’assalam.
Sunana Usman Hussaini Malam Madori, A Jihar Jigawa:
Hakika ya zama dole maza sai muna jin tausayin matanmu, domin dukkanin wani nauyin iyali a kan mu yake sai dai babu laifi idan sun taimaka mana, amma ba dole bane ihsani ne kuma hakan yana kara dankon soyayya. Matsala ce mai girma wanda idan wata bukata ta same ta a lokacin da ba tada shi za ta iya shiga wani hali, don haka ya kamata maza su ke tsayawa a matsayin ginshikin gida masu kula da duk dawainiyar gida. Rashin tausayi da kuma ido a kan abun da take samu ne ya ke jawo haka, wanda kuma hakan sam-sam bai dace ba, domin yana kawo raini a tsakanin mijin da matar ta sa har ma da ‘yan’uwan matarsa. Ba wani abu bane kawai dama su mata an san dawainiyarsu a kan mu take, mu kiyaye domin taimakonsu a kodayaushe, Allah ya sa mu gane hakan.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Daga Jihar Katsina:
Maza da yawa a wannan zamanin sunada wannan gurguwar dabi’a ta sakar wa mata dawainiyar da ba tasu ba. Wanda hakan ke jefa mata cikin mawuyacin hali, kama daga cin bashi dasu buga-buga don ganin dai sun rufa ma kai asiri ta yadda in an kira su za su iya amsawa. A nawa tunanin abun da ke janyo hakan dai mafi akasarin tushen matsalar na ga su matan, su ke wa mazan wannan tarbiyyar basu gane ba. Mace ce in ta ga tana nema tana samu, sai ta dauke wa mijin dawainiyar da duk ya kamata a ce shi ke dauka a matsayinsa na maigida ya kuma saba da hakan. Ita a nata bangaren tana ganin hakan a matsayin kyautatawa ce, shi kuma a na shi bangaren bata bari ya saba da dawainiyar shi ba. Sai tafiya-tai-tafiya abu ya kai makura an tara zuri’a sannan abun ke damunsu, su fara mita da korafin alhalin sune tushen matsalolinsu. Ya kamata mata su gane cewar babu laifi in sun kyautata wa mazajensu, amma su saba masu da daukar dawainiyar da Allah ya daura masu, wanda in gaza wa ce ta yau da kullum ta auku za su iya taimakawa ba tare da gajiyawa ba. Shawarata a nan shi ne; mata su kara ma mazajensu kwarin gwiwar daukar nauyin da ya rataya a kansu, su kara karfafa masu gwiwa a kan neman abun da za su rufa wa kansu asiri, sannan abun da bai zama tilashin su ba, mata su dage da nema ta yadda bani-baninsu ba zai takura ba a wannan yanayin rayuwa da ake ciki. Rannar da gajitawa ta zo sai su taimaka masu a matsayin kyautatawa. Maza kuma masu dabi’ar ganin-gari da ganin kyashi, su kauda idanunsu a kan samun iyalansu, su kula da nauyin da Allah ya basu, in sun kula sun jajirce Allah ba zai taba hana masu yadda za su yi ba. In Allah ya hada mace da mijin mai ganin-gari ita macen sai tai kokarin boye samunta don a zauna lafiya. Allah ya sa mazan da matan duk su gane su gyara.
Sunana Sale Umar Kubuna Malam Madori A Jahar Jigawa:
Magana ta gaskiya wasu mazan basa kyautawa, babu laifi idan mace ta siyi wani abu domin iyali, saboda kyautatawa. Amma namiji shi ne wanda Allah (SWA) ya dorawa nauyi Ci, Sha, tufatarwa, da bukatar rayuwa. Hakan na iya janyo gazawa saboda yau-da-gobe. Yana iya zama dalilin rashin zaman lafiya a zaman takewa, ko kuma ma mutuwar auren, Allah ya kiyaye. Yana iya janyowa raini da sauransu. Rashin wadatar zu ci da son zuciya, lalaci, da kuma karancin ilimin addini da ilimin zamani na daga cikin musabbabin abin da ke janyo hakan. Wannan laifin miji ne dari bisa dari. Mafita ita ce, miji ya dauki nauyin da Allah ya dora masa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakaninsa da iyalinsa, kau da kai a kan abin da matar take samu, da kuma daukar nauyin iyalin gadan-gadan. Su kuma matan su inganta mu’amala tsakaninsu da mazajensu, nuna hakuri da karamci ga mazan.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Kebbi:
Gaskiyar magana wannan al’amari yana faruwa, dan wani namijin daga ranar daya ga samun mace daga wannan lokacin ya ke kokarin boye kudadensa ya zama tamkar marra shi, duk wasu abubuwan na kyautatawa ya daina, a hankali wanda ya zamar masa dole a wuyansa ma wato hakki shi ma ya daina, duk hakan yana faruwa sosai. Ni a nawa tunanin dan mace na sana’a ko tana aiki ba shi ne zai sa ta fi miji kudi ko kuma arziki ba, face ma zai taimaka mata wajen siyen wasu abubuwa wanda in babu sana’ar mijin dai za ta tambaya idan kuwa a kwai sana’a to, kun ga kenan ba sai ta tambaya ba. Misali; kamar gudunmawar biki da ba a rasa mu da shi mata, ga anko, ga kudin dinki, ko na takalmi ko jaka, dole mace na da bukatar wad’annan a rayuwa tunda ba za a ce za ta yi rayuwa da guda daya ba babu karin wata, koda kuwa ba dan biki ba. Amma za a ga namiji ya daina siyan kayan sallah nata dana yaranta, idan kuwa zai yinna yaran to fa iya sallah ne kawai sai salla-salla zai wa yaransa dinki kuma yanada shi ba wai ba shi da shi ba, dan wani ma in ka buncika kudin da yake kashewa a waje dan kawai ya burge wallahi sai ka yi mamaki, cikin gidansa kuma ya bar wa macen ta yi sabida kawai tanada sana’a kamar hakkinta. Shawarar da zan bawa mata su daina nunawa maza adadin abun da suke samu domin watarana ba lalkai su samu hakan ba, sannan duk abin da yake hakkinsa ne muddin ba kida shi kuma yanada shi kar ki soma yi ki kyale. Maza kuma ku ji tsoron Allah domin hakkinku ne idan kun auro yarinya daga gidansu duk wani hakki na uba da zai yi mata to, ya dawo wuyanku koda kuwa da siyen katin waya ne, kudinta nata ne, hakkinku baku ne ba iya ci da sha kawai aka ce ba har da sutura, da sauransu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya daukar nauyin gida a kan mai gida yake duk irin sana’a ko aiki da mace take babu inda addini ya ce ta dauki nauyin gida don haka babu hujja da za ta sa namiji ya bar wa mace ragamar gida a hannunta, sai dai babu laifi idan ta taimaka masa. To magana ta gaskiya hakan yana jawo matar ta raina mijin har yaransu ma su raina shi, domin ya jefar da matsayinsa da Allah ya bashi, kuma zai yi wuya ya iya bawa ‘ya’yansa tarbiyya, kuma ‘yan matar ta sama za su na kallon kamar yana mata kyashi ko baya son ci gabanta. To magana ta gaskiya rashin sanin matsayin aure a addinance ne ya ke kawo haka, domin duk namijin da ya san matsayin aure a musulunci ba zai yi masa rikon sakainar kashi domin ya san Allah zai tambaye shi a kan yadda ya gudanar da gidansa a ranar alkiyama. Laifin namiji ne, domin daukar nauyin gida nashi ne, don haka dole ya yi duk abun da ya dace domin kula da iyalansa, ita kuma mace idan tayi ma kyautata wace ba wai dole ne ba, amma kuma kyautatawa tanada dadi. To hanyar da za a magance wannan matsala shi ne maza su yi karatun addini su san matsayin aure a musulunci da kuma matsayin miji a tsarin zamantakewar aure domin kiyaye matsayinsu, domin aure ibada ne ba a yinsa da’ka dole sai an nemi ilimin da za a gudanar da shi yadda ya dace, daga karshe nake addu’ar Allah ya wadata dukkanin mazaje domin su samu damar daukar nauyin iyalansu yadda ya dace.
Sunana Rahama Musa, Dan zomo Sule Tankarkar A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hakan bai kamata ba, domin daukar nauyin iyali ya rataya ne a kan maigida ko namiji ita mace ba laifi ba ne ta taimaka idan tanada hali amma ba dole ba ne. Yin hakan yana iya haifar da raini a tsakaninsu. abin da yake jawo haka, wasu mazan suna ga idan matansu suka tara kudi da yawa suna fin karfinsu su bada umarni abi, wasu kuma haka nan suke dauke hannunsu a kan bukatun matansu da zarar sun ga sun fara aiki ko sana’a da yawan maza ba sa so su ga matansu da tarin dukiya, wasu kuma sarewa da dora rai. Hanyar da za a magance wannan matsalar; mata su gyara mummunan dabi’arsu idan sun ga sunada dan abin hannu sai su maida miji ba komai ba gaskiya wannan bai kamata ba, kuma duba da wannan yanayin da a ke ciki mace ta goda Allah idan har tanada abin da za ta samu rufin asiri koda miji bai mata ba ki tuna wata mijin ba zai yi ba kuma ba ta da aikin yi ba ta da sana’ar yi sai iyayenta da ‘yan’uwanta za su rika taimaka mata. Hanyar da za a iya magance wannan Matsalar, miji ya ji tsoron Allah, ya tuna matarsa fa amana ce Allah ya bashi don Allah zai tambayeka wannan amanar, idan ka sauke hakkin iyalinka ka fi kima a idonsu ko ba komai a matsayinka na namijin kirki me cikakkiyar daraja bangon gida abin dafawa idan ka bari wani sashi na darajarka ya tabu a idon matarka to ta ya za ka rika bata umarni ta bi, kuma yin haka zai sa ta ji ita ba ta yi dace da jajirtaccen uban ‘ya’ya ba, ka ga hakan abu ne marar kyau. Zaman aure ibada ne sai ana hakuri da juna ga shaidan da yake zagayawa a tsakanin Ubangiji kada mu fi karfin zuciyoyinmu ka bawa maza hanyar da za su ciyar da iyalansu su ma mata Allah ya basu ikon yi wa mazansu biyayya.
Sunana Nura Garba, Dutse a Jihar Jigawa:
Maganar gaskiya daukar nauyin ciyarwa da sharyawa na maigida ne saidai idan Allah ya bawa uwargida arziki za ta iya taimakawa, amma ba wai nauyinta bane tayi hakan, sai dai don Aure abu ne da ya ke bukatar gudunmawar kowa. Zai haifar da raini a tsakaninsu, ta daina ganin girmansa, ko jin maganarsa ko ma ta zama ita ce ke zartar da umarnin komai a gidan, zai zama shugaba a baki amma a zahiri mabiyi ne, domin ya kasa sauke nauyin da aka dora masa. Abubuwan da ke jawo irin haka wani lokacin wasu mazan ba sa amfani da samunsu wajen yin abin da ya zamar musu wajibi, idan ma’aika ne, ko ‘yan kasuwa, wasu suna samun kudi sai dai ka gansu a teburan masu Balangu, Tsire, ko kuma ‘yan matan waje su dinga karbar kudinsa. Gaskiya a tawa mahangar laifin kowannensu ne, laifin namiji shi ne baya kokarin sauke nauyin dake kansa, ko ‘ya’ya yake a matsayin samunsa, ita kuma laifinta bata dauki aure a matsayin hanyar taimakekeniya ba, yadda ta san wataran zai bada kudi tayi abin da bai zama wajibi ba, in ta tallafa sun rufawa kansu asiri ba abin matsala ne ba. Hanyar magnace irin wadannan matsaloli ita ce; na farko, magidanta su dage da neman abin da zai rufa musu asiri, idan kana aiki ka hada da kasuwanci, kuma ya fifita mutunta bukatun iyalinsa fiye da abubuwa marasa muhimmanci, ita kuma ta daina daukar zigar wasu idan an kawo mata domin ta yi wa mijin wani abu, ta dauka komai ta yi masa kyautatawa ce ba komai ba.
Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia A Jihar Jigawa:
Kusan wadannan abubuwan su ke ta faruwa musamman ma a yankunan mu na kabilar hausawa, dan kusan ire-iren wadannan kukan kusan gidaje da dama na ma’auratan ke yi wanda kuma su matan na shiga cikin wani yanayi duk lokacin da ya kasance mazajen sun bar musu dawainiyar nan ta cikin gidan baki daya. Kusan abin da hakan zai iya haifarwa bayan nan abu ne kuma a fili ya ke, duk yayin da aka samu irin hakan daga cikin matsalar da zai haifar a kwai rashin jin maganar shi kansa mahaifin, ita kuma matar za ta zama ita ke juya akalar cikin wannan gidan koda abu bai kamata ba kai matsayinka na wanda baka daukar dawainiyarsu babu ta yadda za ka iya bata umarni ta bi, sai dai za ta iya bin wasu daga cikinsu wasu kuma babu yadda ka iya da ita haka za ka barta ta yi abin da ta ga dama kuma hakan na nuni da cewa cikin fawar da a ka baka ta kula da duk sha’anin gidanta rago sakamakon rashin sauƙewa nauyin da Allah ya dora maka shi. Abin da hakan ke janyowa wasu a kwai karancin sanin miye ne auren kansa da karancin ilimin addini dan idan a kwai wadannan za ka yi duk iya bakin kokarinka wajan ganin ka tsaya a gidanka, sannan kuma ka sauke ire-iren wadannan nauyin da ke kanka ba za ka bar wa mace kaso 70% cikin 100 ba na ayyukanka sai dai ku hadu ku taimakawa juna baki daya ba a barwa bangare daya ba, musamman ma macen wanda ita ba aikin ta ba ne, nata shi ne taimakawa da wasu kananun abubuwa. Maganar gaskiya dai a nan laifin zan iya cewa na mijin ne saboda shi ne jagora kuma lokacin da ya tura waliyyansa wajan daurin aure an shaida masa da cewa shi ne zai samar mata da abin da za ta ci ta sha, sannan kuma ya samarwa da yaransa kulawar da ta kamata idan an samesu, ashe da hakan za mu iya alakanta maganar da laifin a kan mazan. Hanyar kusan daya zuwa biyu ce mazan su yarda da cewa su ne wanda ubangiji ya dorawa wannan hakkin ba matan ba, mata a nan na su shi ne taimakawa da iya abin da za su iya, shawara a nan ita ce mazan su ji tsoron Allah su sani cewa kiwo ubangiji ya basu na matan da iyalan nasu baki daya kuma za a tambaye su shin sun sauƙe kuwa? matan su kuma a nan matukar kina da halin taimakawa mijin naki ki taimaka masa idan kinada shi idan ki ka yi hakan za ki samu ci gaba sosai a rayuwar auren.
Sunana Anas Adamu Malam Maduri (Dan Baba) A Jahar Jigawa:
To hakika ya kamata dukkan mazan da suka san sunada irin wannan dabi’u, da su yi nazari bisa wannan al’amari da budaddiyar zuciya. Su sani cewa ana bada aure ne, da umarnin ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, da sauran dukkan sauran hakkokin aure. Maza na kyale matan da dawainiyar ‘ya’yansu ganin suna wata sana’a koda bata taka kara ta karya ba. Dole Allah zai tambaye mu a kan amanar abin da ya bamu na kiwon iyalan mu. Hakan na haifar da rikici tsakanin iyalanka da sauran mutane gama gari. Domin ‘ya’yan za su ga wani abu daya birge su, amma, ba ta yadda za su samu, zai janyo cin bashi, sata, ko su yi lalaci domin su mallaki wannan abin da suke so. Musamma a ce ‘ya’ya mata ne. Mafi akasari abin da ya ke janyo hakan sakacin iyaye Maza ne. Damin wasu na aurace – aurace su haifi ‘ya’yan kuma su barwa iyaye mata rikon ‘ya’yan koda suna da wadata. Hakan kuma laifin iyaye Maza ne. Domin sakacinsu ne na kula da iyalansu ya janyo hakan. Hanyar da za a bi domin magance wannan matsalar, dola iyaye mata su tilas tawa iyaye Maza kan daukar dawainiyar ‘ya’yansu. Idan sun ki, su kan iya mika al’amarin gurin hukuma domin a kwato musu hakkinsu. Shawarata da zan ba iyaye Maza shi ne; su sani cewa kula da iyali amana ce da Allah ya bamu, kuma zai tambaye mu ranar gobe kiyama. Ya zama dole mu kula, iyaye mata kuma kune kuke tare da yara, ku kuka fi sanin matsalar yaranku, ku yi musu abin da za ku iya, idan ya fi karfinku ku sa iyayensu maza su yi musu.
Sunana Sani Gulle Kampala Malam-madori A Jihar Jigawa:
Hakika duk mijin dake da dabi’a irin wannan na gallazawa matarsa ta-fuskoki makamantan haka to babu shakka ya cika tantagaryar marar tausayi da imani. Domin kuwa matarka ta aure amana ce Allah ya baka har da iyayenta kasancewarsu masu rauni a cikin bil’adama yin irin wannan dabi’ar tamkar gazawa ce kuma ta kan iya kawo raini da farillansa. Eh! to a gaskiya ni dai a ganina irin ababan da ka iya jawo irin wadannan matsalar kamar na-da nasaba da yadda wasu iyayen ke tilastawa ‘ya ‘ya auren dole ko kuma rashin jituwa da ake samu kafinsa a tsakanin bangarorin biyu dake gogayya da juna imma ga iyayen ko ‘ya ‘yansu. To shi dai laifi tudu ne ka take naka ka hango na dan’uwanka kasancewar iya su biyu suke rayuwa a gida yanada wuya tantance mai gaskiya domin da za ka yi alkalanci duk wanda za a barsa ya tsara sai ka hadiyi kur’ani cewa shi ne a kan daidai Allah shi ne ya barwa kansa sani. A gaskiya ya kamata a duk lokacin da ma’aurata suka tsinci kansu cikin irin wannan yanayi a rika kai zuciya nesa gamida kara yin hakuri da juna a kuma ci gaba da fadawa sarki Allah irin halin da a ka tsinci kai a ciki domin shi ne buwayi gagara misali maji rokon bayinsa a ko’ina suke.