Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zamalek da ke ƙasar Masar, ta sallami tsohon kocin Nijeriya, Jose Peseiro, daga aikinsa a matsayin babban kocin ƙungiyar.
An kori Peseiro ne bayan wasan da suka tashi 2-2 da National Bank a gasar lig, wanda ya ƙara jefa ƙungiyar cikin matsin lamba.
Peseiro, ɗan ƙasar Portugal mai shekaru 65, ya karɓi aikin horas da Zamalek a watan Fabrairu kan kwantiragin shekaru biyu, amma bayan shan matsin lamba daga sakamakon rashin nasarori, ɓangarorin biyu sun yanke shawarar raba gari da juna cikin lumana.
“Mun yanke hukuncin raba gari da Jose Peseiro bisa fahimtar juna. Muna yi masa fatan alheri a gaba,” in ji sanarwar kulob ɗin.
Kafin komawarsa Zamalek, Peseiro ne ya jagoranci Super Eagles zuwa wasan ƙarshe na gasar AFCON a Cote d’Ivoire, inda Nijeriya ta sha kashi a hannun ƙasar da ta karɓi baƙuncin gasar.
Daga baya Finidi George ya maye gurbinsa.