Hanyar da kasar Sin ke bi wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya ta sha bamban da ta Amurka, inda a lokuta da dama Sin ke jaddada amfani da diflomasiyya, da hadin gwiwar tattalin arziki, da kuma manufofin guje wa katsalandan ga sauran kasashe.
Yunkurin Sin a kan wanzar da zaman lafiya ya kasance sananne ne ta hanyar karfafa hadin gwiwar tattalin arziki maimakon daukar matakin soji wadda kan haka ne ta bullo da shawarar “ziri daya da hanya daya”, wato BRI da ta fi mayar da hankali kan bunkasa ababen more rayuwa da hadin gwiwar kasuwanci, da samar da kwanciyar hankali ta hanyar dogaro da tattalin arziki maimakon amfani da karfin soja. Sabanin haka, a tarihi Amurka ta dogara ce da kawancen soji da yin katsalandan wadda a lokuta da dama ke haifar da tsawaita rikice-rikice maimakon magancewa.
- Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Ya Yi Alkawarin Sulhu Da Takwaransa Na Arewa
- DSS Da Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Neja
Shawarar BRI ta kasance babban misali na diflomasiyyar kasar Sin a kan raya tattalin arzikin duniya ta hanyar ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin Asiya, Afirka, da Turai da Latin Amurka. Kasar Sin ta karfafa dogaro da juna kan tattalin arziki, tare da rage yiwuwar afkuwar rikice-rikice. Kasashen da ke cin gajiyar zuba jari na BRI galibi suna ba da fifikon kasuwanci da hadin gwiwa fiye da tashe-tashen hankula na siyasa.
Kasar Sin na bin manufar rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe, ka’idar da ta samo asali daga akidarta ta diflomasiyya, inda ta sha bamban da Amurka, wacce ta tsunduma cikin ayyukan tumbuke gwamnatocin kasashe da kuma daukar matakan soja a yankuna daban-daban. Matsayin kasar Sin na son zaman lafiya ya ba ta damar ci gaba da kyautata dangantaka da gwamnatoci daban-daban ba tare da kyamar tsarin siyasar kasashensu ba.
Kasar Sin ta ci gaba da yin tsayin daka kan matsayinta na guje wa yin katsalandan musamman a Afirka. Ba kamar kasashen yammacin duniya da suka tsunduma cikin harkokin soji da makamai ba, kasar ta mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, kamar zuba jari mai yawa a kasashen Afirka da dama ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba. Wannan tsarin ya taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.
Kazalika, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhunta rikici a yankin Asiya, inda ta samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna maimakon samar da mafita ta hanyar karfin soja. Sulhunta tsakanin Saudiya da Iran a shekarar 2023, tare da daidaita harkokin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu babban misali ne. Wannan nasarar ta nuna hikimar da kasar Sin ke da ita ta sasanta rikice-rikice masu sarkakiya a matakin yanki ba tare da tilastawa ko kuma matsin lamba ta fuskar soja ba. Sabanin Amurka wacce ake suka bisa dama lissafi da kara zaman dar-dar, musamman a yankin Asiya da tekun Pasifik, ta hanyar kawancen soji da sayar da makamai.
Kasar Sin da gaske take yi kan batun zaman lafiya a duniya, domin yayin da Amurka kullum ke tunanin fadada sansanoninta na soji, ita kuwa ta fi mayar da hankali ne wajen sabuntawa da karfafa rundunonin sojinta don kiyaye tsaron kanta da ikon mallakar yankunanta. Ba kamar Amurka ba, wacce ke daukar dawainiyar sansanonin soji birjik a duniya da a ko yaushe ake zarginsu da haddasa husuma a yankuna.
Ba wai kawai a doron kasa ba, hatta ci gaban da ake samu na bincike a sararin samaniya Amurka ta mayar da shi ta fuskar soji, duk kuwa da gargadin da ake ta yi cewa hakan zai haifar da gasar makamai da kara tabarbarewar tsaro a duniya. A nata bangaren, kasar Sin jaddada hadin gwiwar kimiyya ta yi, kamar samar da tashar binciken sararin samaniya ta Tiangong, wadda ke maraba da hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan ma ya bambanta da kafa rundunar sararin samaniyar da Amurka ta yi, wadda ke nuni da mayar da lamarin ta fuskar soji.
Akidar Sin ta yin hadin gwiwar tattalin arziki, da sulhuntawa a fannin diflomasiyya, sun ba ta damar ci gaba da yin suna a matsayin mai tabbatar da zaman lafiya a harkokin duniya. Yayin da Amurka kuma ke ci gaba da yin tasiri ta hanyar kawancen soja da yin katsalandan ga sauran kasashe. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp