• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina

by yahuzajere
2 years ago
zaman lafiya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Gutteres ya dauki nauyin samar da wani tsari mai suna “Karfafa Zaman Lafiya a Kananan Hukumomi da Jihohin Katsina da Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya”.

Yankin Arewa maso Yamma, musamman Jihohin Kaduna da Katsina, na fama da matsalolin da suka shafi rikicin manoma da makiya, da rikicin kabilanci da ta’addanci da sauransu.

Domin samun nasarar tsarin, an gudanar da wani taro na musamman a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, ranar Alhamis, don neman goyon baya da tabbatar da zaman lafiya da yaki da ‘yan bindiga musamman a Jihohin Kaduna da Katsina.

  • Dage Takunkumin Canjin Dala Ga Masu Shigo Da Kaya 43 A Sikeli
  • Maulidin Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Reshen Sakkwato Ya Yi Armashi

Babban Jami’in gudanarwa na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, a sanarwar da ya fitar ga manema labarai, ya ce, babban dalilin da ya sa aka kafa Majalisar Dinkin Duniya shi ne samar da zaman lafiya tsakanin kasashe. Domin haka, ya zama wajibi majalisar ta tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a duniya tare da kai ɗauki ga musamman Jihohin Katsina da Kaduna bisa yadda suke buƙatar taimako.

zaman lafiya
Yayin gudanar da taron

A nashi ɓangaren, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda ya bayyana cewa: “A halin yanzu kananan hukumomi 8 da ke maƙotaka da Nijar na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga. Bugu da kari, akwai kananan hukumomi sama da 14 baya ga wadannan 8, da a kowace rana ina samun rahotanni kan hare-haren da ake kai wa kauyuka a cikinsu.”

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

Gwamnan ya kara da cewa: “An dauki jami’an tsaro tare da tura su kauyukan domin dakile hare-haren da ake kaiwa a yankunan”.

Har ila yau, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani wanda mai ba shi shawara na musamman kan samar da zaman lafiya, Atiku Sanke, ya wakilta, ya ba da tabbacin goyon baya wajen ganin an samar da ayyukan da za su tabbatar da zaman lafiya a jihar.

zaman lafiya
Mista Matthias Schmale tare da Gwamna Radda na Katsina

Babbar manufar shirin mai lakabin PBF I4P, ita ce karfafa wa Gwamnatin Jihohin Kaduna da Katsina kwarin gwiwa don samar da hadin kai da hanyoyin zaman lafiya da rigakafin matsalolin da rikice-rikice suke haifawarwa.

Hukumomin da suka hadu wurin samar da wannan sabon tsari na zaman lafiya sun hada da: UNDP, Sashen Kula da Mata na MDD (UN Women), da IOM tare da tallafin Cibiyar OHCHR, domin bayar da gudunmawa ga mutunta hakkin Da’adam.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum
Manyan Labarai

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”
Labarai

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
Manyan Labarai

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Next Post
Wani Matashi Ya Mayar Da Kusan Miliyan 100 Da Aka Turo Asusunsa Na Banki Bisa Kuskure

Wani Matashi Ya Mayar Da Kusan Miliyan 100 Da Aka Turo Asusunsa Na Banki Bisa Kuskure

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.