A yayin da ake murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, mutanen kasashe daban daban sun yabi kasar kan hanyarta ta musamman ta neman zamanantar da kasa. Sai dai ta yaya kasar Sin za ta inganta salonta na zamanantarwa? Kana wadanne damammaki za ta kawo wa duniya? A ranar 30 ga watan da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wurin liyafar bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda ya ba da amsa ga wadannan tambayoyi.
Ta hanyar nazari kan jawabin shugaba Xi, za mu san cewa, damar farko da zamanantarwar kasar Sin za ta haifarwa duniya ta shafi tunanin kasar na kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya. Zamantakewa irin na kasar Sin ta kunshi tunanin neman samun bunkasuwa cikin lumana, kuma ci gaban aikin zai inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya yadda ake bukata.
- Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa A Watan Nuwamba
- Ka Da Mu Yanke Kauna Da Nijeriya – Jonathan
Haka zalika, damar da aikin zamanantar da al’ummar Sin ya haifar, ta ta’allaka ne da yadda tsarin zamanantarwa na Sin zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin dukkan kasashen duniya. A cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya nanata cewa, za a kara zurfafa matakin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, da kokarin sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci. Ta haka, za a samar wa duniya dimbin damammaki don gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu.
A nan gaba, za mu ci gaba da shaida cewa, kasar Sin ba neman zamanatar da kanta kadai take yi ba, maimakon haka tana yin kokari tare da sauran kasashe, don zamanantar da duniya bisa tushen samun ci gaban kasashe cikin lumana, da hadin gwiwa yayin da ake kokarin tabbatar da moriyar juna, gami da samun wadata tare. (Bello Wang)