Kasar Zambia ta gudanar da bikin wayer da kai ga tawagar jami’an lafiya ta Sin ta 26 a kasar, inda jami’an gwamnati suka bayyana godiyarsu ga tallafin da likitocin Sin ke ci gaba da bayarwa wajen karfafa hidimomin kiwon lafiya a kasar.
Da yake jawabi yayin bikin da aka yi jiya, babban sakataren kula da harkokin tallafi na ma’aikatar lafiya ta kasar George Sinyangwe, ya jinjina wa dadadden hadin gwiwar dake tsakanin Zambia da Sin a bangaren kiwon lafiya.
Ya ce jami’an lafiya na kasar Sin sun bayar da gudunmawa sosai ta hanyar jinya da tiyata masu sarkakiya da kula da rashin lafiya mai tsanani da taimakawa wajen ceton rayuka da bunkasa kwarewar jami’ai.
Ya kara da cewa, “ba za mu dauki zuwanku da wasa ba, abu ne mai daraja sosai. Ba kwarewa da dabaru kadai kuka taho da su ba, har da sabuwar mahanga da sabbin dabaru da kwarewa, wadanda za su bunkasa tsarinmu na kiwon lafiya.” (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp