Ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Dr. Dauda Lawal ya ƙaryata jita-jitar da ake yawo da ita na cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP ya koma APC.
Dr. Dauda Lawal shi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP.
A wata takardar sanarwar manema labarai da ofishin yaɗa labaran na Dauda Lawal ya fitar yau Asabar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ya ambaci wannan labari da shiryayyen ƙarya domin a ɓata sunan Dauda Lawal ɗin.
Ofishin ya ce, ba gaskiya ba ne batun cewa Dauda Lawal ya yi wata tattauna ta sirri da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Sani Yarima.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna kira ga dukkanin magoya bayan Gamjin Gusau, Dr. Dauda Lawal, ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ma al’ummar Jihar Zamfara gabaɗaya da su yi watsi da wata jita-jita da ‘yan adawa suke yawo da ita.
“Jita-jitar tasu ta fi kama da wasan yara, saboda suna yawo da ƙaryar wai ɗan takarar Gwamna mai farin jini a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal zai koma APC.
“Wannan lamari bai bamu mamaki ba, saboda mun san jam’iyya mai mulki ba ta da wani abin arziki da za ta iya yin farfaganda da shi, sai dai su dogara da ƙarairayi da sharri don ganin sun dushe hasken Gamjin Gusau.
“Tun bayan da Dauda Lawal ya ayyana aniyarsa ta yin takara suka shiga cikin ruɗani da fargaba. Bayan da ya lashe zaɓen fidda gwanin PDP na Jihar Zamfara, sai hankulansu suka tashi, suka shiga neman hanyoyin yaɗa sharri.
“Ai abu ne ma da hankali ba zai ɗauka ba, a ce mutumin da aka zaɓa a matsayin ɗan takarar gwamna a wata jam’iyya daban ya ajiye takara ya sauya sheƙa. Wannan irin farfaganda ko ƙananan yara ba za su yarda da ita ba. Ko ba komi wannan alamu ne na nasara, cewa jam’iyya mai mulki ta fahimci lokaci ya ƙure mata, kuma tauraron Dauda Lawal ne ke haskawa yanzu a Zamfara.
“Muna yin amfani da wannan dama wurin sanar da al’umma cewa, duk wata sanarwa da ba ta fito kaitsaye daga wurin ɗan takarar gwamna, Dr. Dauda Lawal ko ofishin yaɗa labaransa ba, a yi watsi da ita.” Inji ofishin.