Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Jami’ar Oracle domin saka hannun jari a harkar inganta rayuwar matasa, inganta ƙarfin ma’aikata, da kuma tattalin arziki na zamani a ƙarƙashin shirin Bunƙasa Fasaha na Jami’ar Oracle (SDI).
An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 a Ofisoshin Oracle da ke Landan a Ingila.
- Ko Kun San Dalilin EFCC Na Kama Gudaji Kazaure
- Shugaba Xi Ya Isa Moscow Domin Fara Ziyarar Aiki A Rasha
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, wannan aiki zai samar da haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani ta Zamfara (ZITDA) da Oracle.
Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi.
“Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara, ma’aikata, da tattalin arzikin dijital.
“Makarantar Oracle, shirin ilimi na taimakon jama’a na duniya yana koyar da ilimin fasaha, gami da manhaja da samun damar sanin ilimin fasahar software na kwamfuta ga malamai da ɗalibai a duk duniya.
“Tare da tallafin Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), za a samar da waɗannan albarkatun ga ingantattun manyan makarantu a faɗin Zamfara.”
“ZITDA za ta taimaka wajen jagorantar ayyukan makarantar Oracle Academy a cikin babbar manhajar karatu ta Zamfara, tana ba wa malamai kayan aiki da albarkatun da suke buƙata don koyar da ɗalibai dabarun fasaha da kuma samun takardun ƙwarewa na Oracle.
“Bugu da ƙari, Shirin Jami’ar Oracle (SDI), shiri ne na duniya wanda ke koyar da abubuwa na musamman a duniya ba tare da kashe ko kobo ba ga ɗaliban da suka cancanta, kuma zai ƙara faɗaɗa damarmaki ga ɗalibai a Zamfara.
“Ta hanyar haɗin gwiwar Learning Portal tare da ZITDA, Jami’ar Oracle na shirin ba da damar samun hanyoyin ilmantarwa kyauta da takardun shaida ga mahalartan da suka cancanta a faɗin Zamfara. Wannan ya haɗa da tafiye-tafiye na ilmantarwa wanda ke ba da horo na ƙwarewa na sama da sa’o’i 200 a fannonin da ake buƙata kamar Cloud, Ƙirƙirarriyar Basira ta AI, Data Science da APEX.”
A jawabinsa a wajen rattaba hannu kan muhimmiyar yarjejeniyar, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa haɗin gwiwa da Oracle na daga cikin ƙudirin gwamnatinsa na mayar da jihar Zamfara wata cibiya ta ƙirƙire-ƙirƙire, ilimi, da fasahar zamani.
Ya ce, “A madadin gwamnati da na al’ummar jihar Zamfara, ina miƙa godiya ta ga Oracle bisa yadda ta yi imani da manufofinmu da kuma haɗin kai da mu kan wannan tafiya ta kawo sauyi.”
“Abin da muke yi a yau ya wuce fasaha, samar wa al’umma madogara ne, samar da hanyoyi, da kuma buɗe damarmakin da ke gaba. Ta hanyar saka hannun jari a ilimin dijital, muna ba neman ƙore talauci, rashin aikin yi, da kuma hana yanke ƙauna.”
“Ina godiya ga Oracle don tsayawa tare da mu – yarda da ƙarfin haɗin gwiwa da sanin manufar mu. A yau, ba kawai muna sanya hannu kan takarda ba ne; amma muna yin alƙawari: “Alƙawarin cewa kowane yaro a Zamfara zai samu dama mai kyau don ƙaddanar da burin sa na rayuwa, koyo, da kuma samun nasara. Alƙawarin cewa fasaha za ta zama gadar mu ta zuwa ta samun tattalin arziki mai ƙarfi. Kuma alƙawarin cewa Zamfara ba za ta shiga cikin juyin juya halin dijital kawai ba – a’a mu za mu jagoranci shi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp