Shugaban ma’aikatar kula da haramin Makka da Madina, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya gargadi da kwashin murya ga wadanda ba musulmai ba ke son keta alfarmar haramomin.
Yayi kiran ne bayan ganin wani dan asalin kasar Isra’ila, yana shawagi kusa da dakin ka’aba. Ya kara da cewa duk wanda ya sake keta alfarmar zai fuskanci hukunci mai tsauri.
“Masarautar Saudiyya itace take da cikakken iko da wadannan haramai masu tsarki, saboda haka duk wani wanda ba musulmi ba, da yake kokarin sai ya karya dokar shiga wadannan wurare, lallai baza’a raga masa ba”. Inji Sheikh Sudais.
Gargadin na zuwa ne biyo bayan kama wani dan asalin kasar Saudiyya, wanda ya taimakawa dan kasar Isra’ila shiga cikin birnin haramin Makka.
A wani rahoton shafin Labarun Hausa, tace Hukumar kasar Saudiyyar, sun bayyana tsarkin haraman na Makka da Madina, da cewa wadansu ”jajayen layuka ne,” wadanda ba a yarda wani ya keta su ba in ba Musulmi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp