Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ja kunnen masu daukar doka a hannunsu da wadan da suka mallaki makamai ta haramtacciyar hanya domin samun riba don su haddasa rashin tsaro a kasar nan za su fuskaci Hukunci kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Ya bayyana hakan ranar Alhamis a garin Wudil da ke a jihar Kano yayin bikin yayen dailiban makarantar horas da ‘yan sanda.
- ‘Yan Sanda Sun Ceto Matar Shugaban APC Na Jihar Neja Da Aka Sace A Borno
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Jarumin Nollywood Kan Zargin Yi Wa Karamar Yarinya Fyade
Buhari ya ce, gwamnatinsa zata ci gaba da tabbatar da yakar aikata manyan laifuka a fading kasar nan, shugaban ya umarci ‘yan sandan da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu don ganin an tabbatar da doka da Oda.
Buhari ya ce akwai bukatar a samar da na’urar zamani da za ta taimaka wajen dakile ayyukan masu yin kutse a kafar yanar gizo.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, yankunan Arewa ta tsakiya da kuma a Arewa ta Yamma sun yi nasara wajen rage rikice-rikice da rikicin manoma da makiyaya da satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane.
Ya ce, kai hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram da aikata ayyukan ta’addancin da ‘yan kungiyar IPOB ke yi a wasu sassan Nijeriya da ci gaba da zama barazana ga kasar nan.
Ya ce, gwamnati ta samu nasarar rage ayyukan na su ganin cewa al’amura sun dawo dai dai.