Dan wasan tsakiyar kasar Scotland John McGinn ya ce kasar na da cikakken kwarin giuwa cewa za su iya kawo karshen rashin tabuka abin a zo a gani da kasar ta yi fama da shi a manyan kofunan da ta buga a baya ta hanyar kai wa zagayen gaba a gasar cin kofin nahiyar Turai da ke gudana yanzu haka a kasar Jamus.
Scotland za ta kara da kasar Hungary a Stuttgart ranar Lahadi a wasan karshe na rukunin [A] a gasar Euro 2024, wasan zai kasance mai zafi yayin da duka kasashen biyu ke bukatar nasara domin samun damar kai wa mataki na gaba.
- Kofin Zakarun Turai: Waiwaye Kan Wasannin Da Real Madrid Ta Lashe
- Gasar Euro 2024: Yadda Kasashe Suka Gayyaci ‘Yan Wasa
Sai dai Scotland na da ‘yar fa’ida ganin cewa suna da maki daya a matsayi na uku yayin da Hungary ke mataki na karshe bayan da ta yi rashin nasara a wasanni biyu na farko.
Kasar Scotland na fatan fita daga matakin rukuni a wata babbar gasa a karon farko tun shekarar 1996, shekaru 28 kenan ba tare da ta yin nasara a gasar cin kofin nahiyar Turai ba, koci Steve Clarke ya ce yana sa rai cewar yan wasan na Scotland su fitar da kitse daga wuta a wasansu da kasar Hungary.