Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai bayyana dan takarar da zai goya wa baya a zaben shugaban kasa a watan Janairun 2023.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya ce zai kuma shiga a yi yakin neman zaben dan takarar da ya amince da shi.
- Lewandowski Ya Lashe Kyautar Dan Wasan Da Ya Fi Kowa Yawan Zura Kwallo A Raga
- ‘Yan Daba Sun Hallaka ‘Yansanda 2 A Jihar Kogi
“Daga watan Janairun shekara mai zuwa, zan bayyana wa jama’ata wanda za su zaba,” in ji Wike lokacin da ya kaddamar da gadar sama a karamar hukumar Obio-Akpor a Ribas.
“Saboda haka, kada ku kasance cikin shakku, kuna ta maganganu iri-iri, kuna zagina, ku jira. Janairu yana nan tafe.
“Ba wai kawai zan gaya musu wadanda za su kada wa kuri’a ba kadai, zan tafi jiha zuwa jiha don yakin neman zabe da ni,” in ji shi.
Bayan zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a watan Mayu, inda ya sha kaye, Wike ya shiga takun saka tsakaninsa da Atiku Abubakar kan shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Iyorchia Ayu.
Bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne, adawar ta su ta yi zafi bayan da ya zabi gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.