Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin ceto tattalin arzikin Nijeriya daga durkushewa.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi a taron yakin neman zabensa a Birnin Kebbi na Jihar Kebbi.
- Emmanuel Bwacha Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin APC A Taraba
- Tabbas Jami’an Tsaro Za Su Kare Jami’an Zabe Babu Haufi – Farfesa Yakubu
Ya ce, sana’ar kifi a Jihar Kebbi za ta hade da Legas ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin jihar tare da samar da karin guraben ayyukan yi ga dimbin matasan jihar da ma kasa baki daya.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa zai warware matsalar rashin tsaro da karancin mai a jihar.
Dan takarar, ya nuna jin dadinsa kan yadda dimbin magoya baya suka tarbe shi a jihar.
Ya jinjina wa Gwamna Jihar, Atiku Bagudu da shugabannin jam’iyyar APC na jihar da kuma duk wadanda suka bayar da gudunmawa domin samun nasarar yakin neman zabensa a jihar.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana dimbin jama’ar da suka hallara a wurin taron a matsayin shaida ne na kyakkyawan shugabancin Bagudu a jihar.
A cewarsa, “Mun gamsu da fitowar da muka gani a nan filin wasa na Haliru Audu domin yakin neman zaben shugaban kasa. Wannan shaida ce cewar Jihar Kebbi gidan APC ne. Muna godiya ga jama’a da gwamnatin jihar bisa kokarin da suke yi na ganin taron yakin neman zaben shugaban kasa a Birnin Kebbi ya zama kasance cikin nasara.
“Ina kira gare ku, a yayin da kuke taron gangamin nuna goyon baya ga dan takararmu na shugaban kasa a yau da sauran ‘yan takara, da ku sake fitowa ranar 25 ga watan Fabrairu tare da katin zabenku ku zabi dukkan ‘yan takarar APC, domin Asiwaju Bola Ahmed ya samu nasara,” in ji shi.
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, a jawabinsa ya ce, dandazon jama’ar da suka fito wajen taron wata alama ce cewa APC za ta lashe zabe a jihar da ma kasa baki daya.
Ya kuma yi godiya da goyon bayan da kowa ya ba shi “Ina yi wa dan takarar shugaban kasa da mukarrabansa fatan komawa Abuja lafiya.”