Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta farfado da martabar ilimi a jihar.
Da yake bayar da tabbacin a wajen kaddamar da fara gine-gine da gyaran makarantu a hukumance, Gwamna Lawal ya jaddada kudirinsa na farfado da ilimi.
- ‘Yan fashin Daji Sun Halaka Wasu ‘Yan Sa-kai 6 A Jihar Zamfara
- Dauda Ya Kalubalanci Ganawar Sirri Da Gwamnatin Tarayya Ke Yi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar na baiwa ilimi fifiko domin cika alkawuran yakin neman zabe.
A cewarsa, fara ayyukan ya yi daidai da dokar ta-baci da gwamnatin jihar ta ayyana a fannin ilimi a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp