Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin cewa, a matsayinsa na dan Arewa Maso Gabas mai kuma kishin yankin zai tabbatar an dauki dukkanin matakan da suka dace wajen ganin an fara fito da arzikin Mai da Allah ya albarkaci jihohin Bauchi da Gombe da su muddin aka zabeshi a matsayin shugaban kasa a 2023.
A cewarsa, “Shekara da shekaru ana cewa akwai Mai a Arewa Maso Gabas daga Nijar, yanzu an dawo Bauchi da Gombe, yau ga naku dan Arewa Maso Gabas. Idan kun zabi PDP za mu tabbatar da aikin Man nan an yi shi wannan karon, ba za a rufe mana rijiya a ce a’a ba na Mai ba. Ina son na muku wannan alkawarin insha Allah.”
Atiku wanda ke wannan bayanin a ranar Talata a jihar Bauchi yayin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Bauchi da ya samu halartar dubban jama’a, kana kusoshin jam’iyyar da dama sun halarci gangamin da ya gudana a dandalin wasanni ta Sitadiyum da ke jihar.
Ya kara da cewa, “Mutane su na tambaya wai shin in an debo Mai din nan ta yaya za a fitar da ita, ina son na fada muku cewa za mu farfado da hanyar Jirgin kasa wanda za mu yi amfani da shi ya dibi Mai din nan zuwa inda duk za a kai.”
“Ai ga Nijar su na hakar Mai ko ba su yi ne? Ba su fitar da Mai din? Ai ga Chadi su na hakar Mai, ba su fitar da Mai din ne? To muma muna da hanyoyin da za mu fitar da Mai dinmu insha Allah.”
Atiku ya kara da daukan alkawarin cewa, zai samar da tallafin sana’o’in dogaro da kai ga mata da matasa wanda a cewarsa idan ya zama shugaban kasa zai ware maguden kudade da za a raba ga al’umma a matsayin tallafin sana’o’in dogaro da kai domin fitar da jama’a daga cikin kangin talauci da fatara.
“Za mu fitar da maguden kudade masu yawa da za mu bai wa masu yin sana’a mata da Matasa musamman matasa domin a rage matsalar zaman banza. Don haka ba ku da wata jam’iyya kamar jam’iyyar PDP.”
Ya roki jama’a da su zabi PDP a dukkanin matakai, ya kuma gode kan yadda jama’a suka fito domin nuna masa soyayya da kauna.
Atiku ya ce kusan watanni biyu su na yawon zaga Nijeriya domin yakin zabe amma ba su ga inda aka Allah ya nuna musu yawan mutane kamar jihar Bauchi ba, don haka ya nuna hakan a matsayin karamci sosai da aka masa kuma ya misalta hakan a matsayin alamun nasara.
“Wadanda suke karya suke cewa gwamna Bala Muhammad bai gina PDP a Bauchi ba yau mun zo mun ga yadda Kaura ya gina PDP a Bauchi. Don haka Bauchi sai Bala.
“Bari na gaya muku, kuma ina rokonku duk wani wanda zai zabeni a jihar Bauchi, kai dan PDP ne, kai dan APC ne, kai dan Labour ne, ko kai dan kowace jam’iyya ne, in ka zabeni to ka zabi Kaura.
“Wannan shi ne mutanen APC a da suka zo su na ce mana sak, to yanzu muma za mu ce musu PDP sak, PDP sak daga sama zuwa kasa.”
Shi kuma a nasa jawabin, gwaman jihar Bauchi, Bala Muhammad ya shaida cewar za su fito su zabi Atiku Abubakar ba tare da wani sharadi ba domin sun tabbatar zai ceto Nijeriya daga halin da take ciki.
A cewar Bala Muhammad, “Kai mai gidanmu ne Babanmu ne, ba za mu baka wasu roke-roke ba sai mun kauce za mu gaya maka abubuwan da suka damemu, amma wadannan din ma ba sharadi ba ne. Za mu zabeka ba tare da wani sharadi ba, za mu zabeka ba sai ka bamu komai ba domin kai ne mu, mu ne kai.
“A matsayina na gwamnan Jihar Bauchi ina maka godiya da ka nuna dattako, sauran mutane ma da suka nuna tababa muna rokonka ka gaya musu su su yi biyayya wa nau’in mulki da PDP saboda mu zauna mu ci zabe ba tare da wani hamayya ba.”
Ya bai wa Atiku tabbacin cewa jama’a za su zabe shi a jihar, “Mai girma Wazirin Adamawa Bauchi taka ce, Bauchi ta PDP ne, kuma ba mu da wata miskila. Akwai wasu masu karya su na nuna banbance-banbance a nau’in shugabanci, za mu yi hakuri da su saboda shure-shure baya hana mutuwa.
“Wannan jiha ko ka zo ko baka zo ba, ina tabbatar maka za ka ci zabe a Bauchi fiye da kowace jiha a Nijeriya.”
Ya yi amfani da wannan damar wajen gode wa dandazon wadanda suka sauya sheka daga wasu Jam’iyyu zuwa PDP a jihar, ya nuna hakan da cewa ya kara musu tabbacin samun nasara a zaben da ke tafe.