Sabon Darakta Janar na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Ahmed Musa, ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa domin dawo da martabar ƙungiyar a idon duniya.
Ahmed Musa ya bayyana haka ne a wani taro da ya jagoranta tare da shugabannin ƙungiyar a hedikwatarsu da ke filin wasa na Sani Abacha a Kano.
- ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato
A ranar Asabar da ta gabata ne gwamnatin Jihar Kano ta naɗa shi a matsayin sabon Darakta Janar.
Musa, wanda tsohon kyaftin ne na Super Eagles, ya buga wa Kano Pillars wasa a kakar da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye 10 a cikin wasanni 23 da ya buga.
A wancan lokacin ƙungiyar ta ƙare a matsayi na tara a teburin gasar.
Ahmed Musa ya ce zai buƙaci haɗin kai daga duk masu ruwa da tsaki domin ciyar da ƙungiyar gaba.
Ya kuma ce zai taimaka wajen samar da kayan aiki da tallafin da ƙungiyar ke buƙata domin ta yi fice a sabuwar kakar wasa mai zuwa.
Ya ce: “Ina tabbatar wa kowa cewa da goyon bayanku da na mambobin hukumar, zan yi iya ƙoƙarina don dawo da Kano Pillars matsayin ya kamata a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya.”
Ƙungiyar Kano Pillars, wacce ta taɓa lashe kofin NPFL sau huɗu, ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta shekarar 2025/2026.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp