Sabon zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda, ya sha alwashin riko da akalar jagoranci mai gidansa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Abba, ya yi wannan furuci ne a jawabinsa bayan INEC tabbatar shi a matsayin zababben gwamnan Kano.
- An Gurfanar Da Mamu A Kotu Kan Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci
- Magoya Bayan Peter Obi Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Abuja Kan Zaben 2023
Yayin da yake yi wa mutanen Jihar godiya, da suka danka masa rahamarsu a hannunsa, ya ce zai bai wa mara da kunya.
Ya ce zai gudanar da gwamnatin da za ta fifita maslahar al’umma da kuma kyautata ilimi.
Ya ce al’ummar jihar sun nuna masa kauna a lokacin da yake yakin neman zabe da kuma ranar zabe, duk bai dauki salon amfani da abin duniya ba wajen neman kuri’unsu.
“Muna godiya ga Allah da Ya ba mu wannan nasara.
“Duk da kalubalen da aka fuskanta kama daga tambarin jam’iyyarmu da ya yi dishi-dishi a takardun zabe, da yadda abokan hamayyarmu suka yi amfani da abin duniya don a kada musu kuri’a, ya kara tabbatar mana da cewa ‘Taliya ba ta zabe’.
Ya kara da cewa ba zai yi sako-sako wajen yaki da cin hanci da kyautata rayuwar al’umma ba.
Haka kuma, ya ce zai bayar da fifiko wajen kyautata ilimi da lafiya da kasuwanci da tsaro da harkokin noma.
Sabon gwamnan ya lashe zaben da aka gudanar da kuri’u miliyan 1,019,602, bayan doke babban abokin hamayyarsa, Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya samu kuri’u 890,705.