Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya, ya yi gargadi kan sha’anin tsaro sakamakon zanga-zangar #EndBadGovernance da ke gudana a fadin Nijeriya.Â
Ofishin ya soke dukkanin gurbin wadanda ke neman biza da aka tsara a ranar 1 da 2 ga watan Agusta, 2024.
- Ba Mu Da Hannu A Kisan Isma’il Haniyeh – Amurka
- Kasurgumin Dan Ta’adda Ya Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja da Ofishin Jakadancin Amurka a Legas za su yi aiki ne kawai da ma’aikatan da suka zama wajibi a wadannan ranakun, inda suka shawarci sauran ma’aikatansu su zauna a gida don kauce wa duk wani tashin hankali da zanga-zangar za ta haifar.
Gargadin ya bayyana cewa ana sa ran zanga-zangar za ta fara a wurare daban-daban a Abuja da Legas, kuma za ta iya fantsama zuwa wasu garuruwa.
Ofishin Jakadancin ya yi kashedi kan yiwuwar toshe hanyoyi, cunkoso a tituna, da kuma yiwuwar rikici yayin zanga-zangar.
Har ila yau, akwai fargabar cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda za su iya amfani da damar zanga-zangar don kai hare-hare.
An shawarci ‘yan kasar Amurka da ke Nijeriya su guji wuraren zanga-zanga, su kasance masu lura, suke bibiyar labarai, kuma su zama cikin shirin ko ta kwana.