Kwanan nan batun zanga-zangar da matasa ke yekuwar yi a fadin Nijeriya zuwa karshen watan Yulin da muke ciki ta dauki hankulan al’umma. Malamai, masana da sauran jama’a kowa yana ta tofa albarkacin bakinsa a game da manufar zanga-zangar, wadanda suka kudiri aniyar yi (matasa) da ita kanta zanga-zangar ma.
Ya ku ‘yan uwana ‘yan Nijeriya ku sani: duk irin tsananin halin da muke ciki, wallahi gwara hakan da a ce kasar mu ta yamutse, ta shiga tashin hankali, fada ya barke. Misali, yanzu kasashe irin su Sudan, Syria, Yemen da sauransu, wallahi duk sun gwammace a ce suna cikin irin halin da muke ciki a Nijeriya, da irin yanayin da suka fada na damuwa da yaki da tashin hankali. Don haka matasa a yi hattara, kar mu yarda da duk wanda zai zuga mu mu yi tashin hankali, ko mu kara jefa kasar mu cikin wata damuwa!
- Ba Za Mu Shiga Zanga-zangar Da Za A Yi Wa Tinubu Ba – Daliban Arewa
- Zanga-Zanga Ko Kun San Babban Dalilin Garƙame Abusalma A Kurkuku
Haba ‘yan uwana matasa, to ko a kasashen Turai, inda zanga-zangar ta samo asali, wa ya fada maku cewa duk lokacin da aka yi zanga-zanga sai shugabanni sun yi abin da ake so? Kwanan nan wace irin zanga-zanga ce ba a yi ba a kasashensu, a kan irin cin zalin Falasdinawa da isra’ila take yi, kuma gwamnatocinsu suna bai wa isra’ila makamai? Amma don Allah sun daina abun da suke yi na goyon bayan Isra’ila?
A nan Nijeriya da aka yi zanga-zangar ‘EndSars’ a kasar nan, a kan cin zalin ‘yan sanda, ai an kashe mutane da yawa, an kona dukiyoyi masu tarin yawa, kuma an fasa gidajen yari ‘yan ta’adda da yawa sun fito, sun gudu, sun addabi mutane, amma abin da aka nema na hana cin zalin ‘yan sandan yana nan bai gushe ba. To meye amfanin zanga-zangar kenan? Shin ‘yan Nijeriya don Allah ba za mu hankalta ba?
Tun daga shekarar 2011 dukkanin kasashen da suka yi zanga-zanga wai da sunan zaluncin shugabanni, da wadanda suka yi nasarar kifar da shugabannin, da wadanda ba su yi nasara ba, babu wadanda ba su ce gara jiya da yau ba, babu wadanda zanga-zangar ta warware wa matsalar da suke ciki a kasashensu, duka matsalolin da ake kuka a kan su, wallahi suna nan, kuma zanga-zangar ma ta zo da wasu matsalolin na daban wadanda kafin ta ma babu su. Shin ‘yan Nijeriya ba za mu hankalta ba?
Duk wanda ka ga yana tattauna hukuncin zanga-zanga a addini, idan ka ga ya siffantu da sifa biyu, to ka sani dan son zuciya ne, ba gaskiya yake so ba, siffofin su ne kamar haka: Idan ka ga baya kawo maka Hadisan da Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya hana a yi fito-na-fito ga shugaba saboda wani aikin assha da yake yi, har Hadisin ya siffanta wanda ya mutu a hakan a matsayin wanda ya yi mutuwar jahiliyyah, da Hadisan da suke hana yi wa shugaba nasiha a fili sai a boye.
Na biyu, iIdan ka ga yana kafa maka hujja da abubuwan da suka faru na fitintinu a tsakanin sahabbai, wanda abu ne sananne cewa: ba a sanya cin karo tsakanin maganar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam da aikin wani, ko da kuwa sahabi ne, ballantana abubuwan da suka faru a lokacin fitina, wanda da yawan sahabbai sun kaurace masa saboda ba su gamsu da shi ba.
Masu zuga al’ummah su yi zanga-zanga da sunan addini ya ba da damar a yi, irin su Farfesa Labdo da makamatansa, ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood (Ikwanul Muslimin) da suka damalmala kasashen musulmai, muna fatan Allah ya shirye su, Allah ya kame hannunsu, ya kare al’ummah daga yaudararsu da sharrin da suke yadawa, amin.
Akwai abubuwan da duk mai hankali ba sai an ce masa kar ya yi ba, saboda bayyanar tasirin barnarsu a fili karara, da izina da aka samu kansu, koda wasu gafalallu suna ingiza mutane da suyi!
Mai hankali yana daukar izina ne daga waninsa, ba ya bari ya zama abin daukar izina!
Daga cikin illar zanga-zanga a kasar nan, hatta jami’an tsaron da muke ta kukan sun yi kadan, wadanda suke cikin daji wajen yakar ‘yan ta’adda, da wadanda suke kan manyan hanyoyi, idan har aka fara wannan zanga-zangar ta tsiya, duk hankalin gwamnati zai dawo wajen shawo kan zanga-zangar, a manta da maganar tsaro da ‘yan ta’adda, wanda hakan zai yi mummunar illah ga sha’anin tsaron kasar nan.
Allah yasa mu gane, Allah ya shiryar da mu, amin.
YA KU ‘YAN UWANA ‘YAN NIJERIYA, SHIN ANYA DA GASKE MUNA SON INGANTACCEN SHUGABANCI A KASAR MU KUWA?
Ni dai a iya bincikena, da iya yawon da na yi a duniya, ban taba ganin masu kukan zaluncin shugabanni, kuma wadanda ba da gaske suke yi ba, kamar ‘yan Nijeriya. Dalilai na su ne kamar haka:
- Duk wanda ka ga yana kukan ana zalunci, to mafi yawa bai samu damar a yi zaluncin da shi ba ne, ko kuma da aka yi zaluncin ba a dan sammasa ba ne, ba wai tsabar kyamar zaluncin ba ne da gaske ya sa muke ta ihu. Da zarar an shigar da mutum ciki, to za ka ji ya yi shiru, watakila ma har kare abin zai rika yi, iya in da karfinsa ya kare.
- Duk kukan da ake yi na rashin ingancin shugabanci, idan zabe ya zo, wadannan da ake kuka a kansu, idan sun bayar da atamfa ko taliya, ko kuma sun raba wasu ‘yan kudade, sai ka ga su ake zabe ba wadanda suka cancanta ake zabe ba.
- Babu wanda ke son a fada masa inda tasa matsalar take domin ya gyara, kowa so yake a ce matsalar Nijeriya ta wasu ce ba tashi ba ce.
WATA KILA SABODA BA DA GASKE MUKE YI BA, SHI YA SA KA GA ALLAH YA KYALE MU MUKA SHIGA HALIN DA MUKE CIKI A YAU.
Amma gaskiyar magana, wallahi laifin ba na shugabanni kawai ba ne. Dukkaninmu, kowa ya duba laifinsa, mu gyara, sai Allah ya tausaya muna.