Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar gargadi kan duk wani nau’i na tashin hankali yayin zanga-zangar da ake shirin yi na nuna adawa da tsadar rayuwa da halin kuncin da kasar ke ciki.
Da yake jawabi a wajen taron ’yan kasuwa, masu rike da makaman sarautar gargajiya, da malaman addini a gidan gwamnati ranar Laraba a Kano, Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya.
- Kasar Sin Na Adawa Da Kuma Yin Allah Wadai Da Kisan Gilla
- Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai
“Zanga-zanga ba za ta kai mu ko’ina ba, ina kira ga masu son nuna ‘yancinsu na yin zanga-zanga da su guji yin duk wata dabi’a da bata gari ka iya amfani da ita wajen Barnata dukiyar al’umma,” in ji Yusuf
“Ina mai tabbatar muku da cewa, gwamnati ba za ta amince da duk wani yunkuri na barnata dukiyar al’umma ba, maimakon haka, ina mika goron gayyata ga masu son yin zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji dadin sauraren koke-kokensu tare da samun damar tattaunawa mai ma’ana.”
Gwamna Yusuf ya bayyana kokarin gwamnatin jihar na inganta rayuwar al’ummarta, inda ya jaddada hadin kan Mutanen Kano wajen ganin an samu sauyi mai kyau.
Gwamna Yusuf ya kara da gargadin cewa, duk wani nau’i na tashin hankali ko barna a yayin zanga-zangar, gwamnati ba za ta lamunta ba.
“Ba za a amince da barnatar da dukiyoyin gwamnati da sace-sacen dukiyoyin al’umma ba,” in ji shi.