A daidai lokacin da ake sa ran za a fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Nijeriya a ranar 1 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta ayyana dukkanin gidajen gyara hali 256 da ke fadin Nijeriya a matsayin “jar danja” inda ta yi gargadin cewa, kada a keta alfarmar su a kowane irin hali.
Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Gidajen fursuna na Kasa (NCoS), Halliru Nababa, ne ya yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, ACC Abubakar Danlami Umar, ya sanya wa hannu a madadinsa ranar Talata a Abuja.
- Hukumar Siyasar Kwamitin Tsakiyar JKS Ya Kira Taron Nazarin Yanayin Tattalin Arziki
- Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar
Nababa ya bayyana cewa, “Saboda zanga-zangar da aka ce za a gudanar a ranar farko ta watan Agustan 2024, hukumar kula da gidan gyara hali ta Nijeriya na son sanar da jama’a cewa, an sanya duk gidajen gyara hali na Nijeriya a matsayin ‘jar danja’; don haka, duk wani mutum ko gungun mutanen da ba su da hurumi, kar a gansu a wuraren.”
Hukumar da ke kula da gidajen gyara hali ta Nijeriya ta bukaci jama’a da su ba da hadin kai wajen kiyaye dukiyoyi da lafiyar al’umma.
Sanarwar ta kara da cewa, an samar da isassun matakan tsaro domin tabbatar da cewa, babu wani gidan gyara hali da aka kai wa hari.