Yau Talata, hukumar siyasar kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kira taro, domin bincike da yin nazari kan yanayin tattalin arzikin kasa, yayin da ta shirya ayyukan tattalin arziki na rabin karshe na shekarar bana. Kuma babban sakataren kwamitin tsakiyar JKS Xi Jinping ya jagoranci taron.
A taron, an jaddada cewa, ana fatan habaka bukatun al’ummun kasa ta hanyar farfado da harkokin yin sayayya, da kuma mai da hankali kan tallafawa al’umma da inganta harkokin yin sayayya a lokacin da ake tsara manufofin tattalin arziki. Kana, ya kamata a dukufa wajen raya sabbin sana’o’i da kuma sana’o’in da za su sami babbar bunkasuwa a nan gaba, yayin da ake karfafa aikin bude kofa ga waje, da kuma ciyar da aikin farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni gaba, da kare sakamakon da aka cimma a fannin kawar da talauci. Haka zalika kuma, ana fatan tafiyar da aikin samar da guraben aikin yi ga daliban da suka kammala karatunsu a jami’o’i yadda ya kamata, yayin da ake aiwatar da aikin tinkarar ambaliyar ruwa, gami da aikin ceto yadda ake bukata. (Mai Fassara: Maryam Yang)